1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Red Cross ta koma bakin aiki

Ramatu Garba Baba
September 15, 2019

Kungiyar agaji ta kasa da kasa Red Cross ta koma aikin bayar da agaji da sahalewar Kungiyar Taliban mai rike da yankuna da dama na kasar Afganistan.

https://p.dw.com/p/3Pctz
Afghanistan Südkorea Geiseln werden freigelassen Rotes Kreuz
Hoto: AP

Roya Musawi, mai magana da yawun kungiyar ta Red Cross ta ce tuni aka soma gudanar da aikin jin kai a duk fadin kasar bayan samun tabbacin tsaro daga kungiyar mai karfin iko. Ayyukan Red Cross, sun hada da kwashe gawarwaki da aka bari a fagen daga ya zuwa bayar da kulawa da magunguna ga mabukata da kuma shirya ziyara a tsakanin fursunoni da iyalansu.

A watan Afrilun 2018, Red Cross ta dakatar da aikin ceton, bayan da kungiyar Taliban da ke rike da ikon yankunan da dama a Afganistan din, ta ce ta janye kariya da ta bata, wanda ke nufin ba lallai bane ta yi la'akari da kasancewarsu a wuri in har ta shirya kai hari. Wannan dai na zuwa ne a yayin da Shugaban Amirka Donald Trump ya yi watsi da batun tattaunawar zaman lafiya da kungiyar masu tayar da kayar bayan da ake fatan ka iya kawo karshen zubda jini a kasar.