Aikin tsara gwamnati a Afghanistan
August 21, 2021Jami'in ya ce kwararrun masana na kungiyar na can na aiki tukuru wurin fito da tsarin shari'a da addini da kuma manufofin kasa da kasa wanda Taliban za ta yi amfani da shi wurin tafiyar da gwamnatinta tare da hulda da kasashen duniya.
Rahotannin da ke shigowa na cewa babban jigon kafa kungiyar ta Taliban Abdul Ghani Baradar ya isa birnin Kabul a yunkuri na kafa gwamnati.
A gefe guda kungiyar ta Taliban ta ce ta cimma yarjejeniya da kasashen yamma a game da yadda za su kwashe mutanensu a kasar cikin kwanciyar hankali.
Tun daga karshen makon da ya gabata dai, Taliban ta ci gaba da nanata cewa mulkinta zai kasance mai cike da sassauci a wannan karon sabanin mulki mai tsauri da ta yi a tsakanin shekara ta 1996 zuwa 2001 a kasar ta Afghanistan kafin Amurka ta hambarar da ita.