1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taliban ta hana haske fim dauke da mata

November 22, 2021

Ma'aikatar inganta kyawawan dabi'u ta gwamnatin Taliban a Afganistan ta ce kafafen talabjin na kasar su daina watsa duk wani wasan kwaikwayon da ke dauke da mata 'yan wasa.

https://p.dw.com/p/43Jv3
Afghanistan Symbolbild Bildung Frauen
Hoto: Majid Saeedi/Getty Images

Sabuwar dokar dai na zama irinta ta farko ga kafafen talabijin din kasar. Hakan dai na zuwa ne bayan da Taliban ta dauki alkawarin kasancewa mai matsakaicin ra'ayi a wajen gudanar da mulkinta. Kazalika kungiyar ta dakatar da haske duk wani shirin film da bai kunshe da koyarwar addininin musulumci da kuma wanda ya sabawa manufofin gwamnatin kasar ta yanzu. A cewar wani kakakin kungiyar, duk wata 'yar jarida da ke aiki a kafar talabijin wajibi ne ta sanya hijabi, koda yake ya tabbatar wa da kamfanin dilancin labaran Spaniya cewa dokokin ba wajibi bane amma akwai bukatar a kiyaye su yayin watsa shiri.

Tun dai a watan Augustan da ya gabata ne dai kungiyar ta Taliban ta karbi ikon Afganistan bayan hambarar da ita gomman shekarun da suka gabata.