Taliban ta haramtawa gidajen talabijin amfani da bidiyo
October 15, 2024Gidajen Talabijin biyu da ke lardin kudancin kasar sun fara aiwatar da haramcin gwamnatin kasar na daina amfani da hotuna a kafafen talabijin domin kaucewa fushin jami'an hukumar hisba da ke bibiyar kafafen yada labaran domin ladabtarwa.
karin bayani: Shekaru uku da dawowar Taliban kan mulki
Wani 'dan jaridar kamfanin dillancin labarai na AFP a lardin Takhar ya rawaito cewa gidan talabijin na Mah-e-Naw ya gudanar da labarai ba tare da amfani da hotunan bidiyo ba, inda suka yi amfani da labule mai dauke da rubutu da kuma muryoyi.
karin bayani: Taliban ta haramta wa mata zuwa makaranta a karo na uku
Mai magana da yawun ma'aikatar tabbatar da da'a a tsakanin al'ummar kasar ta Afghanistan Saiful Islam Khyber, ya shaida wa manema labarai cewa wannan mataki na daga cikin manufofin gwamnatin Taliban na amfani da koyarwar addinin Islama a kasar.