An kafa gwamnatin wucin gadi a Afghanistan
September 7, 2021A wata ganawa da manema labarai a wannan yammaci a birnin Kabul, kakakin kungiyar Zabihullah Mujahid ya kuma bayyana cewa an nada Mullah Abdul Ghani Baradar a matsayin mataimakin firaminista haka kuma Maulawi Mohammad Yaqoob Mujahid zai rike mukamin ma'aikatar tsaron kasa, kana kuma Alhaj Mullah Serajuddin Haqqani zai kasance ministan cikin gida a yayin da Maulawi Amir Khan Muttaqi kuwa zai jagoranci ma'aikatar harkokin waje.
Kungiyar ta girmama tsoffin jiga-jiganta da suka yi gwagwarmaya ta tsawon shekaru 20 bayan tunbukesu daga jagorancin Afghanistan ta hanyar nada wasu daga cikinsu a manyan mukamai, ciki har da shugaban gwamnati Mohammad Hassan Akhund da ya kasance tsohon gwamna a Kabul yayin mulkin kungiyar, haka shima Mullah Abdul Ghani Baradar, na daga cikin na gaba gaba da suka jagopranci tattaunawar ficewar Amirka daga Afghanistan.