1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taliban ta kai hari a birnin Kabul

Yusuf Bala Nayaya
August 21, 2018

A wannan rana ta Talata, an jiyo kararraki na ababen fashewa a yankin da jami'an diflomasiya ke gudanar da harkokinsu a birnin Kabul fadar gwamnatin Afganistan.

https://p.dw.com/p/33S62
Afghanistan Raketenangriff auf Kabul
Hoto: Reuters/M. Ismail

Babu dai wasu bayanai da ke nuna cewa hare-haren sun ritsa da wani ko wani ya samu rauni kamar yadda shedu da jami'an tsaro suka fada wa kamfanin dillancin labarai na Reuters.

Wani jami'in tsaro ya ce fashe-fashen sun biyo bayan wasu makaman roka da aka harbo daga wajen birnin na Kabul. Wasu rahotannin na cewa mayakan Taliban ne suka harba makaman da suka nufi fadar shugaban kasa. Harin da ke zuwa a lokacin da Shugaba Ashraf Ghani ke jawabin barka da sallah ga al'ummar Afganistan.

Mayakan Taliban sun yi watsi da bukatar da gwamnatin kasar ta Afganistan ta gabatar masu ta neman tsagaita wuta tun daga ranar Litinin wato ranar Arafat har zuwa lokacin watan Mauludi inda kungiyar ta sha alwashin ci gaba da kai hare-hare kan jami'an gwamnati da kawayensu na kasashen ketare.