1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rikici ya rincabe a Afghanistan

Ramatu Garba Baba
August 1, 2021

Mayakan Taliban sun kai wasu hare-hare da rokoki kan filin jirgin sama da ke Kandahar wanda shi ne birni na biyu mafi girma a kasar Afghanistan.

https://p.dw.com/p/3yNlk
Afghanistan Kandahar Airbase
Hoto: MIKE PATTERSON/AFP/Getty Images

Rahotanni daga kasar Afghanistan na cewa, mayakan Taliban sun harba wasu rokoki filin jirgin saman kasar da ke a Kandahar, birni na biyu mafi girma a kasar, lamarin da tuni ya saka mahukunta soke soke tafiye-tafiye. Wannan na zuwa ne a yayin da mayakan Taliban ke kara matsa kaimi tare da fadada iko a manyan biranen kasar, da kuma zafafa hare-hare da suke kai wa muhinman gina-ginan gwamnati.

Fadan da ake a tsakanin rundunar gwamnati da ta Taliban ta janyo asarar rayuka da dukiya tare da tilastawa dubbai tserewa gidajensu. Shekaru ashirin da suka gabata rundunar sojin hadaka da Amirka ke jagoranta ta shiga kasar da zummar taimaka ma rundunar gwamnatin kasar murkushe Taliban, amma ba tare da tayi nasara ba, daga karshe Amirkan da abokan ta sun yanke shawarar barin kasar.