1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taliban ta kai hari kan sojojin NATO

Ramatu Garba Baba
August 2, 2017

Kungiyar Taliban ta kai hari kan ayarin sojojin NATO da ke a birnin Kandahar na kasar Afghanistan kwana guda da kai harin da ya hallaka mutane 26 da kuma raunata wasu fiye da 60.

https://p.dw.com/p/2hZbN
Afghanistan Kandahar - NATO Convoy angegriffen
Hoto: picture-alliance/abaca/A. Sana

A kasar Afghanistan, mayakan kungiyar Taliban sun kai wani kazamin hari a kan ayarin motocin dakarun tsaro ta NATO a birnin Kandahar; rahotanni a kasar na cewa sojoji da dama sun jikkata duk da cewa babu sanarwa a kan adadin mutanen da lamarin na wannan Larabar ya shafa, sai dai kakakin rundunar sojan kungiyar kawancen da ke kasar ya tabbatar da aukuwar harin a kan ayarin motocin na NATO ya kuma ce tabbas akwai wasu da dama da suka sami rauni amman bai kai ga bayyana sunayensu ko asalin kasashensu ba.

Harin na yau na zuwa ne a yayin da ake shirin gudanar da jana'izar wasu mutane 29 da suka rasa rayukansu a harin nan da aka kai a wannan Talata a tsakiyar masallacin 'yan shi'a a daidai lokacin da jama'a ke shirin yin Sallah, Kungiyar IS mai da'awar Jihadi ta dauki alhakin kai hari na jiya da ya yi sanadiyar rayuka da dama kuma raunata wasu mutane fiye da sittin, a baya kungiyar ta IS ta fitar da sanarwar inda a ciki ta yi gargadin cewa tana shirin kai hari kan 'yan mazhabar shi'a a kasar ta Afghanistan.