1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Afghanistan: Taliban na kara kwace yankuna

Abdoulaye Mamane Amadou
August 12, 2021

A cigaba da yunkurinta na mamaye Afghanistan kungiyar Taliban ta karbe iko da binrin Ghazni birni na biyu mafi girma da ke Kudu maso yammacin Kabul.

https://p.dw.com/p/3ysE7
Afghanistan | Taliban-Kämpfer | Stadt Farah
Hoto: Mohammad Asif Khan/AP/picture alliance

Wani jami'i a ma'ikatar yankin Ghazni mai Nasir Ahmed Faqiri, ya sheda wa kamfanin dillacin labarai na AFP da cewar yanzu hakan 'yan Taliban ne ke rike da fadar gwamnan yankin da barikin 'yan sanda hakan nan da gidan yari, sai dai yace har yanzu kungiyar na ci gaba da gwabza yaki da dakarun gwamnati a wasu sassa.

Masu sharhi dai na ganin faduwar birnin Ghanzni mai tazarar kilo mita 150 kacal daga birnin Kabul, ka iya zama wata kafa ta shigar 'yan kungiyar zuwa Kabul babban birnin Afghanistan.

Shugaba Recep Tayyip Erdogan na Turkiya a wata hira da tashar talabijin ta CNN, yace a shirye yake ya gana da jagoran kungiyar 'yan Taliban da yanzu haka ke rike da kaso daya daga cikin uku na manyan biranen kasar Afghanistan.