1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taliban ta yi bakin ganga kan zaman lafiya

Mouhamadou Awal Balarabe
December 30, 2019

'Yan Taliban sun yi alkawari rage fitintinun da suke haddasawa a kasar Afghanistan maimakon tsagaita bude wuta kwata kwata kamar yadda Amirka ta bukata. Sassa biyu na neman farfado da tattaunawa tsakaninsu.

https://p.dw.com/p/3VUXW
Afghanistan Taliban
Hoto: picture-alliance/NurPhoto/M.S. Shayeq

Kungiyar Taliban ta bayyana cewar ba ta da niyar tsagaita wuta a Afghanistan sakamakon tattaunawar wanzar da zaman lafiya da take yi da Amirka. Sai dai cikin sanarwa da ta fitar a birnin kabu,l kungiyar da ke da tsaurin kishin Islama ta ce abin da za ta iya yi kawai shi ne sassauta tashe-tashen hankulan da take hadasawa. Dama tattaunawa tsakanin bangarorin biyu kan batun janyewar sojojin Amirka daga Afghanistan ta tsaya cik, sakamakon harin da kungiyar Taliban ta kai kan sansanin sojoji a farkon watan Disamba.

Wannan tattaunawar ta tanadi "rage tashin hankali," da ta kai kololuwarta a watan Satumba lokacin da Shugaba Donald Trump na Amirka ya dakatar da ita, bayan wani harin ta'addanci da ya kashe sojojin Amirkan biyu. Sassa biyu sun sake komawa kan teburin tattaunawa kafin a sake dakatar da sulhun bayan wani hari kan barikin soja na Bagram, wanda sojojin Amirka ke kula da shi. Sannan kungiyar Taliban ta dauki alhakin wani sabon hari a ranar Litinin din da ta gabata, wanda ya kashe wani sojin Amirka daya.