Manyan kasashe ba za su amince da gwamnatin Taliban ba
September 3, 2021Ministocin harkokin wajen kasashen Tarayyar Turai sun amince da ci gaba da tattaunawa da mayakan Taliban da suka wkace madafun ikon Afghansitan, amma ba za su amince halarcin da gwamnatin da mayakan za su kafa ba, kamar yadda babban jami'in kula da harkokin kasashen ketere na kungiyar, Joseph Borrell ya tabbatar a wannan Jumma'a lokacin taron a kasar Slovaniya. Haka kasar Birtaniya ta kawar da yuwuwar za ta amince da halarcin gwamnatin da Taliban za ta kafa.
Haka na zuwa lokacin da wasu majiyoyi daga mayakan Taliban ke cewa Mullah Baradar daya daga cikin wadanda suka kafa kungiyar zai jagorancin gwamnatin da za a kafa. Kana 'yan kungiyar za su nada ministocin ma'aikatu 25. Mayakan Taliban sun kwace madafun iko bayan Shugaba Ashraf Ghani ya tsere ranar 15 ga watan jiya na Agusta daga kasar.
Har yanzu akwai yankin tsaunikan Panjshir da ke hannun masu adawa da Taliban wanda kuma ke zama tungar tsaffin mayakan Northern Alliance, inda yanzu haka suke ci gaba da fafatawa da mayakan Taliban tare da kin mika wuya. Mayakan da ke nuna tirjiya ga Taliban sun hada da tsaffin sojojin gwamnatin da ta rushe. Duk gwamnatin da za a kafa tana da gagarumin aikin magance matsalolin tattalin arzikin a kasar ta Afghanistan wadda ta dogara kan taimakon kasashen duniya da yanzu suka zuba ido domin ganin abin da zai faru.