1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tallafin ceto ga Spain

September 11, 2012

Ba zan karbi tallafin ceton tattalin arziki da aka jinginawa sharuda ba:- inji Rajoy

https://p.dw.com/p/166YK
Source News Feed: EMEA Picture Service ,Germany Picture Service Spanish Prime Minister Mariano Rajoy poses after arriving for an interview on national Spanish Public Television (TVE) in Madrid September 10, 2012. REUTERS/Susana Vera (SPAIN - Tags: POLITICS)
Hoto: Reuters

Firaministan Spain Mariano Rajoy yace bai yanke shawara ba tukunna ko kasarsa za ta nemi cikakken tallafin ceton kungiyar tarayyar turai. A hirarsa ta farko a Talabijin tun bayan da ya dare karagar mulki a watan Disanbar bara, Rajoy yace ba zai karbi tallafin ceton tattalin arziki wanda aka jinginawa wasu sharuda ba. Ya yi nuni musamman da shirin Fansho wanda yace ko kadan ba zai lamunta da rage masa kudi ba domin karbar tallafi. Tuni dai kasar Spain ta karbi tallafin kimanin euro biliyan dari na euro domin taimakawa ceto bankunan kasar daga durkushewa. Domin saka karimcin da aka yiwa kasar Firaminista Rajoy ya amince da daukar katakan tsuke bakin aljihun gwamnati wanda ya hada da karin haraji akan abin da mutum kan biya daga ribar da ya samu da kuma karin haraji akan kayayyakin da ake sayarwa.

Mawallafi: Abdullahi Tanko Bala
Edita: Saleh Umar Saleh