1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Nijar: Tallafin makamai daga Turai

Gazali Abdou Tasawa LMJ
November 28, 2022

Gwamnatin Jamus da kungiyar Tarayyar Turai EU sun bai wa Jamhuriyar Nijar tallafin kayan yaki da suka hada da motoci da kuma na'urorin sadarwa, a wani mataki na taimakon sojojin kasar a yaki da ta'addanci.

https://p.dw.com/p/4KC5O
Nijar | Tsaro | Tallafi | Jamus | EU
Tallafin tsaro ga jami'an sojojin NijarHoto: picture-alliance/Zuma/A. Fox Echols Iii

Tuni dai kungiyoyin adawa da zaman sojojin kasashen ketare a kasar suka fara tofa albarkacin bakinsu, kan yadda kasashen na Turai suka fara mayar da hankali ga taimakon Jamhuriyar ta Nijar da kayan yaki maimakon jibge sojojinsu. Gwamnatin ta Jamus da kungiyar ta EU sun bayar da tallafin wadannan kayan yaki ne ga rundunar jami'an tsaron kasa ta Garde Nationale a karkashin wani shiri na neman wanzar da zaman lafiya a yankuna masu fama da matsalar tsaro,  wanda aka fi sani da Projet de Stabilisation wanda Hukumar Raya Kasashe ta Majalisar Dinkin Duniya wato UNDP ke kula da shi. 

Nijar | Sojoji | Tsaro | Ta'addanci | Horo
Horo ga sojojin NijarHoto: Gazali Abdou

Da yake tsokaci kan wadannan kayayyaki da Jamus da kungiyar ta EU suka bai wa jami'an tsaron na Nijar, mai sharhi kan harkokin tsaro a kasar Malam Alakassoum Abdourahmane ya ce kayan da aka samu za su yi tasiri sosai ga inganta harkokin sadarwa a tsakanin jami'an tsaron kasar musamman a fagen daga. Tuni dai kungiyar Tournons La Page wacce ke adawa da jibge sojojin ketare a Nijar, ta bakin shugabanta Maicon Zodi ta bayyana gamsuwarta da taimakon wanda ta ce shi Nijar ke bukata a yaki da ta'addanci ba jibge mata sojoji na ketare. Wannan dai shi ne tallafin kayan yaki kusan na hudu da Nijar ta samu daga kasaashen Turai da Amirka, cikin kasa da watanni uku wanda ke zuwa a daidai lokacin da manyan kasashen duniyar ke raba gari da kasar Mali da kuma soma nazarin ficewa daga Burkina Faso.