Hukumomi a Jamus na son a agaji kasashe masu raunin arziki
March 12, 2022Talla
A yayin wata hira da jaridar "Augsburger Allgemeinen" ministar raya kasa ta nan Jamus Svenja Schulze, ta ce yana da muhammanci a karfafa taimakon kasa da kasa ga kasashe masu karamin karfe da ke dogaro da kayayakin abincin da Rasha da Ukraine ke samar wa don karesu daga fadawa cikin matsalar yunwa.
Wasu alkaluman Kungiyar Tarayyar Turai dai sun yi nuni da cewa a shekarar da tagabata, Rasha ce kasa ta farko a duniya ta fi kowace samar da garin alkama a yayin da ita kuwa Ukraine ke da matsayi na biyar a jerin kasashen duniya da ke samar da alkama. Ministar ta ci gaba da cewa rikicin Ukraine da Rasha ka iya janyo wa kasashen ma da suka ci gaba mummunar matsala da barazana ga fagen dimukradiyyarsu.