Ko wanene Sanoussi Jackou?
July 19, 2022An haifi Sanoussi Tambari Jackou a garin Kornaka da ke cikin gundumar Dakoro a jihar Maradi. Marigayi Sanoussi Jackou ya kasance dan gidan sautar Kornaka, bayan ya soma aikin gwamnati a shekara ta 1970 sai shekaru shida baya, sakamakon wani yunkurin juyin mulki da bai yi nasara ba a ranar 15 ga watan Maris na 1976.
An zargi marigayin da hannu a cikin yunkurin juyin mulkin, wanda har ta kai shi ga dauri a gidan yari da gwamnatin mulkin soja ta Janar Seyni Kountche ta masa na tsawon shekaru 11. Bayan da Allah ya ma Shugaba Kountche rasuwa, an sallami Jackou daga gidan yari a ranar 23 ga watan Nuwamba na 1987. Sanoussi Jackou ya sake komawa kan aikin gwamnati a shekara ta 1988.
A shekara 1990 Sanoussi Jackou ya kasance memba a kwamitin koli na jam'iyyar siyasa CDS Rahama, daya daga cikin jam'iyyun farko da aka assasa bayan sakin mara ga tafarkin dimukuradiyya.
Ya zama dan majalisar dokoki a karkashin inuwar wannan jam'iyyar a watan Faibrairun 1993 lokacin shugaba Mahamane Ousmane ne ke tafiyar da jagorancin Nijar kuma dan jam'iyyar siyasa daya da marigayi Jackou. Shugaba Mahamane Ousmane ne na farko a tsarin dimukuradiyyar Nijar mai jam'iyyu barkatai, an zabe shi a matsayin mataimakin shugaban majalisar dokoki har zuwa shekara 1994.
Bayan da Janar Ibrahim Baare Mainasara ya kifar da gwamnatin farar hula mai tattare da cece-kuce, marigayi Sanoussi Jackou ya karbi mukamin ministan ilimi mai zurfi, inda ya fice daga jam'iyyarsa ta CDS-Rahama.
Ya kafa ta shi jam'iyyar ta PNA-Al'umma a shekara ta 1997don gwagwarmaya ta siyasa. Mutuwar Ibrahim Bare Mainasara ta jefa Tambari Jackou a kawancen 'yan adawa, a shekarar 2004 ya yiwa surukinshi tsohon shugaban Nijar Mamadou Tandja adawa ta tsawon shekaru biyar.
Ya zama dan majalisar dokoki a karkashin inuwar jam'iyyar PNA Al'umma, ya wakilci yankin Maradi a majalisar a shekara ta 2009, kuma tun daga wacan lokaci Jackou ke kusa a kawancen jam'iyyun da ke mulkin Nijar.
An nada shi mukamai da dama ciki har da mai ba wa shugaban kasa shawara na musamman a fadar gwamnati har tsawon shekaru 10. Bayan da Mohamed Bazoum ya dare kan kujerar mulki, ya sake nada marigayin a matsayin mashawarci da ke iya kai korafinsa a kololuwar mulkin kasa kama daga fadar shugaban kasar har ta firaminista.
Ya rasu yana da shekaru 82. Ya bar mata daya Bafarashiya da ya auro tun lokacin da yake karatu a Faransa, kuma suna da 'ya'ya hudu, ciki har da wacce ta taba rike mukamin minista da kuma babbar jami'a a hukumar yaki da masassarar cizon sauro ta kasa.