1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tanka ta kashe mutane 140 a Pakistan

June 25, 2017

Rahotannin da ke fitowa daga Pakistan na cewa sama da mutane 140 suka mutu bayan faduwar wata tankar mai a kan hanyar Karachi zuwa Lahore a lardin Punjab na kasar.

https://p.dw.com/p/2fKtn
Screenshot Twitter Usman Dar
Hoto: Quelle Twitter/Usman Dar

Da safiyar wannan Lahadi ne dai lamarin ya faru, kuma mutanen da suka mutu a hadarin sun gamu da ajalinsu, lokacin da suke kwasar man fetur da ke zuba daga motar, wadda daga bisani ta kama da wuta. Akwai wasu mutanen sama da 100 da suka sami munanan kuna a lamarin. Motar ta fadi ne da litar man fetur dubu 40, a kusa da birnin Bahawalpur, cikin lardin Punjab.

A halin da ake ciki dai jami'an agaji na can suna kwashe gawarwakin da wutar ta yi matukar lalata su, wasu ma ba a iya shaida su. Ana kuma bayyana cewa wadanda za su rasa rayukansu ka iya karuwa saboda munin yanayi da wadanda suka ji rauni ke ciki.

Dabi'ar kwasar ganima dai ba sabuwar aba ba ce a wasu yankunan kasar ta Pakistan musamman wadanda ke fama da matsanancin talauci, inda akasari mata da matasa a wasu lokutan har da kananan yara ke amfani da irin wannan yanayi wajen samun kudade.