Kasar Tanzaniya za ta kara ciwo bashi
January 21, 2022Wannan cece-kuce dai ya samo asali ne daga lokacin da shugabar kasar Tanzaniya Samia Suluhu Hassan ta ce gwamnati za ta ci gaba karbar bashi daga kasashen ketare, domin gudanar da ayyukan ci-gaban kasa. A cewar babban bankin kasar, daga watan Nuwambar shekarar da ta gabata kasar ta ciwo basusuka da suka hada da na ciki da wajen kasar a kanta da suka kai kimanin dalar Amirka miliyan dubu 28. An dai yi amfani da kudin ne wajen gudanar da ayyukan layin dogo daga birnin Dar es-Salaam zuwa Morogoro-Dodoma da kuma aikin samar da hasken wutar lantarki a Rufiji, dukkansu a yankin gabar teku. A baya-bayan nan Shugaba Suluhu Hassan ta ce karbar bashi daga ketare ba sabon abu ba ne a Tanzaniya.
Jawabin shugabar dai ya haifar da zazzafar muhawara a kasar, inda masana tattalin arziki ke kumfar baki tare da gargadin kasar kan illar hakan. Duk da cewa akwai tarin bashin da suke kan kasar har kawo yanzu, 'yan kasar na bayyana mabambantan ra'ayoyi kan hakikancewa da gwmanati ke yi, domin kara laftawa kanta wasu basussukan. Shugaban majalisar dokokin kasar Tanzaniyan Job Ndugai ne dai ya kunna wutar muhawarar da ta barke a kasar, bayan murabus din da ya yi sandiyar matsin lambar da ya ke samu daga magoya bayan jam'iyyar CCM mai mulki da suke ganin ya na yi wa gwamnatin Shugaba Samia Suluhu Hassan zagon kasa.