Tanzaniya ta soke bukuwan ranar 'yanci
December 9, 2022Shugabar kasar Tanzaniya, Samia Suluhu Hassan ta soke bukukuwan ranar 'yancin kai da za a yi a yau Juma'a, tana mai ba da umurnin yin amfani da kudaden da aka ware domin ranar wajen gina dakunan kwana ga daliban da ke makarantu na masu bukata ta musamman.
Bikin na cikar kasar ta Tanzaniya shekaru 61 da samun 'yancin kan, da ma an ware masa kudade ne da suka kai dala dubu 445.
Tuni ma dai gwamnatin ta ce aka rarraba kudaden domin fara aikin gina dakuna ga daliban a fadin kasar ta Tanzaniya da ke a gabashin Afirka.
Da ma dai an saba shirya kasaitaccen biki a lokacin muranr samun 'yancin kan a kasar, kuma ba wannan ne karon farko da ake soke shi.
A shekara ta 2015 ma, gwamnatin marigayi Shugaba John Magufuli ta yi hakan, inda aka yi amfani da kudaden wajen gina hanyoyi a birnin Dar es Salaam, kamar yadda a 2020 aka yi amfani da kudaden wajen sayen kayayyakin kiwon lafiya.