Tanzaniya: Wayar da kan yara masu fama da nakasa
May 11, 2016A shekara ta 2015, cibiyar Charity Sightsavers ta fidda rahoton da ya nuna cewar akalla yara miliyan 23 da ke fama da nakasa a duniya ba sa samun damar yin karatu ko da matakin firamare. Don ganin an taimaka wa wannan rukuni na yara, wani malami a birnin Arusha da ke gabashin kasar Tanzaniya, Loy Yamat ya kfa kungiyar HACRET wata karamar kungiya mai zaman kanta da ke wayar da kai.
Yawancin daliban da Loy Yamat ke koyar da su a wani aji da bude, kurame ne. To sai dai yana amfani da yatsuntsa ne dan kwatance wajen koya wa daliban yadda za su furta harafin "A". Shekarun baya ne dai, ya dasa tubalin cimma burinsa, ya kuma fara ne a wani kango ba tare da tallafin wasu malamai ba.
Ganin yadda ake nuna wa masu nakasa kyama da kushe, ya sa Loy Yamat ya kirkiro kungiyar HACRET mai zaman kanta don gina wasu ajujuwan da zimmar kawo sauyi a zukatan iyayen da ke tauye hakkin yara da ke da nakasa a Tanzaniya.
“Masu nakasa na fama da kalubale da dama. Musamman a bangaren ilimi, akalla yara kashi 90 cikin 100 ba sa makaranta a Tanzaniya."
Kyama daga dangi da 'yan uwa
Wani babban kalubale shi ne yadda masu nakasar ke fuskantar kyamata mai tsanani daga danginsu na jini.
Jessica Mwakatundu ta zama saniyar ware a tsakanin danginta har ma mijinta, sakamakon Allah Ya jarabci danta mai suna Gideon da cutar tabin hankali. To amma Jessica Mwakatundu ta ce wannan makaranta ta kawo sauyi ga rayuwar dan nata a yanzu.
“Akwai canji sosai, a baya ba ya sanin wane ne shi balle ya san me yake yi. Amma da ya fara halartar wannan makaranta sannu a hankali yana dawowa cikin hayyacinsa.”
A yanzu dai burin wannan malami shi ne yadda daliban za su koyi gudanar da rayuwarsu kamar kowa. Kuma bisa ga dukkan alamu, kwalliya na biyan kudin sabulu kamar yadda wata daliba mai suna Mwishimu Dadiana ke bayyana burinta a nan gaba.
“Ina da burin in cigaba da karatuna har zuwa matakin sakandare, sannan idan dama ta samu sai na cimma jami'a.”
Shi dai Loy Yamat na kan bakansa na ganin ya sauya ra'ayi ga masu akidar kyamatar masu nakasa.