1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tarayyar Turai za ta cire takunkumi da ke kan Iran

Suleiman BabayoOctober 16, 2015

Cire takunkumin yana da nasaba da yarjejeniyar da aka amince da tsanin manyan kasashen duniya da Iran.

https://p.dw.com/p/1GpZK
Ayatollah Seyed Ali Khamenei
Hoto: Leader.ir

Akwai yuwuwar Tarayyar Turai za ta bayyana kawo karshen takunkumin karya tattalin arziki da ta saka wa Iran ranar Lahadi mai zuwa, kamar yadda wasu majiyoyin diplomasiya suka tabbatar.

Kasashen Yammaci sun saka takunkumin bisa tsoron kasar ta Iran za ta yi amfani da shirin bunkasa makashin nukiya wajen kera makamai. Matakin cire takunkumin zai fara aiki zuwa karshen shekara, idan Iran ta fara cika sharuddan da aka amince da su yayin yarjejeniyar da kasar ta kulla da sauran manyan kasashen duniya, bayan Tarayyar Turai ta samu tabbaci daga hukumar kula da makamashin nukiliya ta Majalisar Dinkin Duniya.

A wani labarin Amirka ta ce kwajin makami mai linzami da Iran ta yi ya saba kudirin Majalisar Dinkin Duniya. A cikin wata sanarwa Jakadiyar Amirka a majalisar Samantha Power ta ce ranar 10 ga wannan wata na Oktoba Iran ta yi kwajin makamin mai tafiyar matsakaicin zango.