Tarihin gine-gine na Jamus ta Gabas
An sami habakar gine-gine bayan yaki a bangaren Jamus ta Gabas, ci gaba da kasar da jam'iyyar Gurguzu suka yi fata. Wadannan gine-gine sun kasance masu kyau da kuma suka zo bisa tsari daban-daban kuma masu kayatarwa.
Stalinallee na gabashin Berlin a shekara ta 1953
"A shirye don aiki da kare zaman lafiya," wannan shi ne abin da ke a rubuce a kan allon da ake gani makale cikin katagon nan da ke yankin Stalinallee a Berlin a 1953. Tsarin ya kuma kunshi manufar 'yan gurguzun Jamus. Raba irin wadannan gine-gine da siyasa a yankin Jamus ta Gabas , abu ne da ba zai yiwu ba.
1956-1959: Habakar kamfanoni da gidaje a yankin Pirna
A shekarun 1950, Jamus ta Gabas ta gina wajen hada injunan jirage a wajen da ake kira Pirna kusa da birnin Dresden a cikin matakai na sirri. An kuma gina wajen cin abinci domin bukatar ma'aikata. An kawata ginin da hanyoyin hawa bene masu kyawun gaske, duk kuma a bayan yakin. A yau, wannan ginin ya koma rukunin kyawawan gidaje na alfarma.
Tashar jirgin kasa na Potsdam tsakanin 1956-1958
Saboda kusacin yankin da yammacin Berlin, wadanda suka tsara Jamus ta Gabas suka yi layin dogo da ya hada yankin da Postdam. Hakan ya sa aka tsara tashar ta zama mai layuka da dama da kuma babban zauren karbar matafiya da aka bude a shekarar 1958. Ta kasance har zuwa 1961, kafin gina katanga. Sai dai tashar ta rasa matsayin bayan samun sauyi na siyasa a Jamus ta Gabas.
Sinima ta matasa a Frankfurt a shekarun 1954-1955
An samar da gidan Sinima na Matasa (Lichtspieltheater der Jugend) a birnin Frankfurt a tsakiyar shekarar 1950, ginin da daga bisani ya koma cibiyar dabbaka al'ada. An yi wa ginin zanen "Trümmerfrau" (matar da ta taimaka wajen gina wajen bayan yaki) kuma ma'ikaciyar kamfanin karafa. An ci gaba da amfani wajen da kyawunsa har zuwa shekara ta 1998.
Ginin hukumar kididdiga a gabashin Berlin a shekarar 1969
Jamus ta Gabas ta gina sabuwar cibiyarta a Berlin. Sai dai a shekarar 1957 an inganta sginin zuwa tsari na ci gaban zamani. An samar da dogayen manyan binayen da aka gina da karafa da kuma wannan Eriyar tashar talabijin da ake iya gani a tsakiyar wajen da ake kira 'Alexanderplatz'. Tashar ce ta kuma sanar da dakile nasarar jam'iyyar masu ''ra'ayin gurguzu'' a lokacin.
Kamfanin hada kayan laturoni a gabashin Berlin tsakanin 1967-1969
Gidan kayan laturoni, kamar yadda ake kiran wajen. Tsaye a tsarin shekarun baya na gine-gine masu kayatarwa a gabashin Berlin da ke yankin Jamus ta Gabas. Akwai ma wajen tafiye-tafiye a wani bangare na ginin. Wannan benen na kusa ne da Alexanderplatz ne gabashin na Berlin. Dukkanin gine-ginen na tsaye har yanzu, ana kuma aiki a cikinsu.
1969-1971: Gidan tafiye-tafiye (Haus des Reisens) a gabashin Berlin
Har i zuwa lokacin da Jamus ta hade, nan ne babbar cibiyar sayar da tikitin tafiye-tafiye a yankin Jamus ta Gabas. A ciki ne ofisoshin da ke sayar da tikitin jiragen sama da na kasa suke. An kawata ofisoshin da kayan alatu a ciki da kuma rubuce-rubuce masu karin haske ga matafiya. A halin yanzu dai ginin na zaman babban gida adana tarihi.
Gidan Sinima (Rundkino) a birnin Dresden a shekarun 1970-1972
Wannan gidan sinima na Dresden, wani gwanin zanen taswirar gine-gine Manfred Fasold da Winfried Sziegoleit ne suka gina shi da nufin kawata harabar titin Prager. Daga ciki akwai manyan wuraren haska fina-finai guda biyu. An lalata wasu sassan ciki lokacin yaki. Yanzu dai yana daga cikin muhimman gine-ginen zamani, bayan yakin.
1986-1988 Music Pavilion, Sassnitz
Katafaren tanti na gabar ruwan Baltic da Sassnitz ke a ciki, waje ne da ke tsibirin Rügen, waje ne na nishadi da debe kewa. Fasihin zane-zanen taswirar gine-gine Ulrich Müther daga yankin Binzne ya gina shi a gabashin Jamus. Müther da aka haifa 1934 ya mutu a shekarar 2007. Yanzu dai ana kula da wajen a matsayin muhimmin waje na tarihi.
Arewacin garin Rostock mai tarihi a shekarar 1983-1987
An fara gine-gine a shekarar 1983 a dogon babban titin birnin Rostock cikin tsarin gini mai karfi na zamani. Toh amma, sai magina a yankin suka koma tsarin gini irin na gargajiya wanda ba ya bukatar nazari mai yawa. Daga cikin tsarin na gargajiya, ana amfani bulo na kasa da galibi ake amfani da shi a Jamus maimakon na sumunti da ake gani kala-kala a yau.