Tarihin Masallacin Agadez a Jamhoriyar Nijar
June 4, 2012Masallacin Juma'a ta Agadez, tun kafa Agadez aka yi shi, ya faɗi aka sake zuwa aka gina shi, bayan da ya faɗi ne aka ɗauko wani mallami mai suna Zakariya. Sarkin Agadez na wancan lokacin, ya nemi shi ya ce cikin amanar Allah ya zo ya yi mishi Masallaci na juma'a, kasancewar dama can shi ya yi na Timbuktu da na Gao. Mallam Zakariya ya amince ya gina masallacin amma bisa sharradin cewa za'a tara mutane su kawo sadaka saboda Allah ba tare da an matsa masu ba. Haka kuwa aka yi mutane suka taru suka bada sadaka. Wannan waliyin ya ɗauki lokacinsa ya gina wannan masallaci. Ya ce duk wanda ya ga faɗuwar wannan masallaci zai ga tashin ƙiyama
Yadda aka gina Masallacin
Wasu suna raɗe-raɗin cewa daga an tashi da safe sai a ga ana cigaba da gina masallaci, ba'a sanin ainihin yadda ake yi, amma Mohammed Bilal wani masanin tarihi, ya ce wannan zance ne kawai na mutane, shi dai bawan Allahn ya sa an kawo sadaka duka, lokacin da ake aikin, akwai sanhuna wadanda ake zuba laka ana badawa, sa'an nan da fodannai da ake ɗaurawa duniya duk bata san da irin wannan ba, har Ubangiji Allah ya sa aka yi shi. To sai dai ya ce ba zai iya bada tabbacin cewa daga gari ya waye ake ganin mutane na gini ba shi dai jagorar ginin abun da ya ce kawai shine wanda ya ga faɗuwar ginin, zai ga tashin ƙiyama.
Tsarin ginin Masallacin
Kakanni wadanda suka ga mulkin aƙalla sarakuna bakwai a wancan lokacin, suka bada wannan bayanan, inda suka ce akwai matattakala wanda ake hawanta a yi kirar sallah kafin Liman ya zo.
A ƙarƙashinta kuma akwai wata rijiya wadda bakin mambari ne wanda aka aza wani abu, yadda kafin a ƙare Liman yana iya zama.
Duk waɗannan an yi su ne bisa tsari na daa wanda ba kowa bane zai iya fayyacewa. A wancan lokacin ne ma aka yi wani aljani da ya riƙa hawa matattakalan yana kashe mutane, sai Ladani 40 su mutu a yini guda kafin a yi sallar Juma'a. Lokacin bayin Allah ne da dama suka taru suka riƙa addu'a, har Allah ya basu iko, a wani hawa da ɗayansu ya yi yana kira sai ya tsage cikin aljanin, aka ce jinin ya zubo kan wani gurbi wanda aka rufe shi a ciki har ya zamana ana iya zama a kai. Mutane sun kuma sami tarihin wannan aljani a gidajen da ake koyar da karatu ko kuma samun abinci da kuma gidajen sarauta.
Shekarun Masallacin
Wasu na cewa masallacin na da shekaru 700 zuwa 800. Daɗaɗɗen wuri ne saboda Abzin ta daɗe dukka. An yi abubuwan tarihi kamar naɗin sarauta duk a gaban idon abzin. Saboda tarihi ya nuna cewa cikin sarautar abzine Shehu Ɗan Fodio ya yi sarautar Sokoto, daga sarautar Sokoto aka yi ta Kano. Shi Shehu Usmanu Mujadadi da farko sai da ya je ƙasar Abzine inda akwai ƙanin mahaifiyarsa Mallam Mohammad Sambo shi ya fara koya masa karatu, amma daga baya, akwai wani mallami mai suna Jibril, wanda ya cigaba da yi masa karatu. Wannan masallaci kafin zuwan manyan naurorin sadarwa shine akan yi amfani da shi wajen kwatance, tamkar tambari ne na ƙasar Abzine.
Mawallafa: Tilla Amadu/ Pinaɗo Abdu
Edita: Usman Shehu Usman