1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

tarihin Merkel

November 21, 2005

Merkel zata kasance mace ta farko da ta shugabacin gwamnatin Jamus

https://p.dw.com/p/Bu44
Angela Merkel
Angela MerkelHoto: AP

Bayan zabe na gaba da wa’adin da aka gudanar a cikin watan satumban da ya wuce, an ji daga bakin shugaban gwamnati mai barin gado Gerhard Schröder yana mai fadin cewar har abada jam’iyyarsa ta Social Democrats ba zata yarda ta shiga inuwar wata gwamnati ta hadin guiwa da zata kasance karkashin shugabancin Angela Merkel ba. Wannan furuci na Schröder kuwa ba kome ba ne illa wata manufa ta cin mutunci da tsokanar fada ga Angela Merkel, wacce ta lashe zaben da aka gudanar tare da rinjayen da bai taka kara ya karya ba. To sai dai kuma, bayan hali na rudu da rashin sanin tabbas da ta shiga, jami’ar siyasar ta sake yunkura sakamakon goyan bayan da ta samu daga ‘ya’yan jam’iyyarta tana mai bayyana shirinta na jan ragamar duk wata gwamnati ta hadin guiwa da za a kafa, inda take cewar:

Za a ci gaba da tabbatar da hadin kan kasar nan karkashin ka’idojin mulkin demokradiyya, kamar yadda aka saba a cikin tarihinta na wanzuwa tun fil-azal, daidai yadda muka gada daga magabatanmu, wadanda suka dora kasar akan wannan turba ta demokradiyya.

To sai dai kuma ita Merklel, mai shekaru 51 da haifuwa, duka-duka abin da ta sani a game da magabatan da suka dora Jamus kan tsarin mulkin demokradiyya ta nakalce shi ne ko dai daga litattafai na tarihi ko kuma daga tsinci fadi. Domin kuwa ita Merkel ta taso ne a can Jamus ta gabas a wancan zamani. Amma duk da haka bata yi wata-wata ba wajen rikidewa domin rungumar akidar siyasar marigayi Konrad Adenauer da Helmut Kohl bayan shigarta karkashin tutar jam’iyyar Christian Democratic Union (CDU) a shekarar 1990. A ganinta, a wannan marra da muke ciki yanzun, ita wata jami’ar siyasar ce ta kasa baki daya. Merkel ba ta yi wata wata ba wajen amfani da damar da ta samu a gare ta dangane da wargajewar kasar Jamus ta Gabas domin kutsa kai a harkar siyasa inda aka nada ta mataimakiyar kakakin gwamnatin P/M Lothar de Maiziere, wadda ita ce ta demokradiyya ta farko da aka nada a wannan yanki akan hanyar sake hadewar yankunan gabaci da yammacin Jamus. Bayan sake hadewar, Merkel ta cimma nasarar shiga majalisar ministocin gwamnatin Helmut Kohl, wanda aka ce shi ne ya ba ta cikakken goyan baya domin nadinta babbar sakatariyar jam’iyyar kafin ya bar gado a shekarar 1998. Kazalika ita ce ta farko da tayi matsin lamba wajen ganin lalle sai an tsage gaskiya dangane da tabargazar nan ta gudummawar kudi ga jam’iyyar, tana mai bijire wa Kohl, wanda shi ne ke da alhakin wannan tabargazar da ta shafa wa CDU kashin kaza. Wannan karfin zuciyar da ta nunar shi ne ya share mata hanya a sana’arta ta siyasa zuwa ga mukamin shugaban gwamnatin Jamus.