1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tarihin rayuwar Angela Merkel

Babangida Salihu JibrilNovember 6, 2009

Angela Merkel ta hau karagar shugabancin jamus a shekara ta 2005

https://p.dw.com/p/KPmj
Shugabar Gwamnatin Jamus Angela Merkel.Hoto: AP

Ita dai Angela Merkel shugabar gwamnatin jamus an haife ta ne a Garin Hamburg a ranar 17 ga watan julin shekarar 1954, kuma sunanta na ainihi shine Angela Dorothe Kasner. Mahaifinta wani Pastor ne mai bin ɗarikar Protestant a yayinda mahaifiyar ta kuma malamar makaranta ce dake koyar da harshen Ingilishi da harshen Latin.

To sai dai kuma Merkel ta tashi ne a wani ƙaramin gari dake arewa da birnin Berlin dake gabashin jamus, bayan da mahaifin ta yayi hijirah zuwa jamus ta gabas. Merkel wanda ke makaranta a lokacin ta rinƙa yin taka tsantsan wajen kalaman ta, domin gudun kada kalaman nata ya shafi dangantakar dake tsakanin mahaifin ta da kuma gwamnatin gabashin jamus na wancan lokaci.

A lokacin da take jami'ar Leipzig, Merkel ta kasance mai ƙwazo da kuma basira tsakanin tsararrakin ta a jami'a, abinda yasa a lokacin data shiga jami'a ta karanta fannin ilimin Physicst, inda kuma ta samu shedar karatu ta Dakta wato digirin digirgir a shekarar 1978. Kuma kafin ta shiga harkokin siyasa ta fara aiki ne da wata cibiyar binciken harkokin kimiyya ta gabashin jamus daga shekarar 1978 zuwa 1990.

Daga shekarar 1990 ne kuma Angela Merkel, wanda akewa kirarin mace mai kamar maza, ta ajiye harkar koyarwa ta shiga siyasa gadan gadan. Inda kuma ta shiga jam'iyar Christian Democratic Union na tsohon shugaban gwamnatin Jamus Helmut Kohl, a matsayin 'yar majalisa. Kuma bayan nasarar da jami'yar ta samu ne a wannan zaɓe aka naɗa ta ministan kula da jin daɗin mata da matasa da kuma ministan Muhalli.

Amma kuma bayan da jam'iyar tasha kayi a zaɓen 1998. Sai ta zama babbar sakatariyar jam'iyar ta CDU. kana kuma ta zama shugabar Jam'iyar a shekara ta 2000. Kuma kamar yadda tsarin jam'iyun siyasa yake anan jamus, shugaban jam'iya shine ɗan takarar jami'ya a zaɓen ƙasa, don haka ta zama 'yar takarar neman zama shugabar gwamnatin jamus a zaɓen shekara ta 2002, sai dai "kash" jamusawa basu zaɓe ta ba. To sai dai a zaɓen shekara ta 2005, Merkel da jam'iyar ta ta CDU sun samu nasara akan shugaba maici a wancan lokaci, wato Gerhard Schröder, amma da kyar da kujeru uku kacal a majlisar dokoki. Wannan nema yasa aka ƙulla ƙawance tsakanin jam'iyar ta ta CDU da kuma SPD. Bayan wannan ƙawance ne aka zaɓe ta a matsayin shugabar gwamnatin jamus kuma mace ta farko a tarihin jamus kuma mafi ƙarancin shekaru data jagoranci ƙasar. Sannan a zaɓen da aka gudanar na kwanan nan, an sake zaɓen ta domin jagorantar ƙasar jamus na tsawon shekaru huɗu masu zuwa.

Bayan wannan tuta da Angela Merkel ta cira a cikin gida, a ƙasashen waje ma ta ciri tutoci:domin kuwa mujallar Forbes dake bayani akan masu kuɗi da kuma ƙarfin iko a duniya ta bayyana ta a matsayin macen data fi ƙarfin ikon faɗa aji a duniya. kuma tabi sahun tsohuwar Firaminstan Ingila Margaret thatcher da Kim Campbell Firaministan Kanada da Indirah Ghandi na Indiya da sukayi gogayya da maza a ƙungiyar ƙasashen duniya daban daban da suka haɗa da ƙungiyar ƙasashe masu ƙarfin tattalin arziki na G8. kuma bayan haka ta taɓa jagorantar ƙungiyar EU, bayan zama wakiliya a majalisar mata ta duniya masu riƙe da ragamar shugabancin ƙasashen su. Kafin auren ta na fari ya mutu a 1982 sunan mijinta na fari dai shine Ulrich Merkel. Koda yake daga bisani ta sake aure, inda ta auri wani shehun malamin jami'a Joachim Sauer, Angela Merkel dai bata taɓa haihuwa ba, amma tana da ƙanne biyu Marcus na miji da kuma Irene mace, kuma tanajin harshen Rashanci kamar yakin Rasha da kuma harshen Ingilishi.

Mawallafi:Babangida Jibril

Edita:Abdullahi Tanko Bala