1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tarihin saban shugaban ƙasar Ghana John Dramani Mahama

August 6, 2012

John Dramani Mahama mai shekaru 53 a duniya ya riƙe muƙamai daban-daban kamin ya zama shugaban ƙasar Ghana bayan mutuwar John Atta Mills

https://p.dw.com/p/15kes
Ghana's Vice-President John Dramani Mahama (C) sits after taking the oath of office as head of state, hours after the announcement of the death of Ghana's President John Atta Mills, in the capital Accra, July 24, 2012. Mills, who won international praise for presiding over a stable model democracy in Africa, died suddenly on Tuesday and his vice-president was quickly sworn in to replace him at the helm of the oil, gold and cocoa producer. Mahama, 53, will serve as caretaker president until the elections at the end of the year. REUTERS/Yaw Bibini (GHANA - Tags: POLITICS ELECTIONS TPX IMAGES OF THE DAY)
Rantsar da John Dramani MahamaHoto: Reuters

An haifi John Dramani Mahama ranar 29 ga watan Nowemba na shekara 1958, wato yanzu yana da shekaru 53 kenan a duniya.An haife shi awani gari mai suna Damongo.Mahaifinsa Emmanuel Adama Mahama shine dan majalisa na farko mazabar yankinsu kuma shine komishina na farko, wanda ya fito daga yankin mazaɓar da suke tun zamanin jamhuriya ta farko, kenan siyasa John Dramani Mahama tamkar gado yayi daga mahaifinsa.

John Dramani Mahama yayi karatun firamari a makarantar Achitoma School, kamin daga bisani ya shiga makarantar sakandari a Tamale dake arewancin ƙasar.

Ya shga jami'ar Ghana inda ya samu digri ta fannin tarihi a shekara 1981,sannan ya samu wani digirin ta fannin ilimin sadarawa a shekara 1986

Daga nan Mahama ya ci gaba da karatu a birnin Mosko na ƙasar Rasha, a makarantar ilimin zamantakewar al'uma.

Ya dawo gida Ghana a shekara 1991, inda tsawan shekaru biyar yayi aiki a matsayin jami'in hulɗa da jama'a a ofishin jikadancin Japan a birnin Accra na ƙasar Ghana.

Bayan shekaru biyar ya na wannan yanki sai kuma a shekara 1996 ya shiga aiki a ƙungiyoyi masu zaman kansu.Ya yi aiki a ƙungiyar nan mai suna "PLAN International" ofishinta na Ghana, nan ma yayi aiki a matsayin jami'in hulɗa da jama'a.

Ghana President John Atta Mills attends the Symposium on Global Agriculture and Food Security at the Chicago Council on Global Affairs, Friday, May 18, 2012, at the Ronald Reagan Building in Washington. (Foto:J. Scott Applewhite/AP/dapd)
Marigayi John Atta MillsHoto: dapd

Tun yaushe John Dramani Mama ya shiga harakokin siyasa har ta kai shi ga zama shugaban ƙasa?

John Dramani Mahama ya shiga gadan-gadan cikin siyasa lokacin da ya shiga takara a zaɓen 'yan majalisar dokoki na shekara 1996 inda ya samu nasara na wa'adin shekaru huɗu,sanna shekara 1997 aka naɗa shi mataimakin ministan sadarwa na Ghana, zamanin mulkin shugaba Jerry Rawlings,kamin daga bisani ya zama ministan sadarawa gaba ɗaya a shekara 1998.ya riƙe wanna matsayi har zuwa shekara 2001 lokacin da aka kada jam'iyar NDC daga zaɓen shugaban ƙasa.A lokacin da ya na ministan sadarwa, shine kuma shugaban hukumar sadarawa ta ƙasa wadda a ƙarƙashin jagorancinsa, Ghana ta ƙaddamar da shirye-shirye da dama na inganta harkokin sadarawa mussamman yaɗuwa wayar tafi da gidanka.

So uku ya na shiga takara a zaɓen 'yan majalisa kuma ya na yin nasara zama ɗan majalisa, wannan na nuna goyan bayan dake gare shi a mazaɓarsa ta Bole/Bamboi.

A cikin majalisar ma ya riƙe muƙamai daban-daban,misali ya zama kakanin rukunin 'yan majalisa marasa rinjaye daga shekara 2001 zuwa 2002, kuma jam'iyarsa ta NDC ta zaɓe shi a matsayin babban darakta mai kula da harkokin sadarwa.

John Dramani Mahama ya yi zama memba a majalisar dokokin ƙasashen Afrika wada ke da cibiyarta a birninPretoriya na Afrika ta Kudu, a wannan Majalisa ta Afrika,ya riƙe da matsayin shugaban gungun ƙasashen yankin yammacin Afirka.Sai kuma tun daga ranar tara ga watan Janairu na shekara 2009, ya zama mataimakin shugaban ƙasa.Ya riƙe wannan matsayi har zuwa 24 ga watann Juli inda Allah ya karɓi ran shugaban ƙasar Ghana John Atta Mills, kamar yadda kundin tsarin mulkin ƙasar yayi tanadi an rantsar da shi a matsayin shugaban ƙasa domin cika wa'adin mariganyin har lokacin da za a shirya zaɓe.

mit den Orten Nkawkaw, Koforidua und der Hauptstadt Accra eingezeichnet
Hoto: DW

Bayan mutuwar shugaban ƙasar Ghana, rukunin jam'iyu masu riƙe da ragamar mulki, sun yarje akan cewa saban shugaban wato John Dramani Mahama, zai kasance ɗan takararsu a zaɓen shugaban ƙasa da za a shiryawa a ƙarshen wannan shekara a ƙarƙashin tutar jam'iyar NDC.

Iyalin John Dramani Mahama nawa, mi ya fi bashi shawa a zamantakewa?

Saban shugaban ƙasar Ghana na da mata mai suna Lordina Mahama, suna da 'ya'ya bakwai.Ta fannin addini shi mabiya addinin kirista ne, amma a zuri'arsu akwai cuɗaya tsakanin musulmi da kirista.

Ya na da shawar kare mahali mussamman game da matsalolin gurbatar yanayi a Afrika.A lokacin da ya na matsayin mataimakin shugaban ƙasa, an ce ya duƙufa ƙwarai game da wannan batu.

Mawallafi: Yahouza Sadissou Madobi
Edita: Mohammad Nasiru Awal