Tarihin shirin samar da sulhu a yankin Gabas ta Tsakiya
Kusan shekaru 50 kenan bayan yakin kwanaki shida a 1967, sai dai har yanzu an kasa warware rikin Isra'ila da Palasdinu. Ga dan gajeren tarihin kokarin da aka yi don samar da masalaha.
Kudurin kwamitin sulhu na 242, 1967
Kudurin kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya na 242, da aka zartar a ranar 22 ga watan Nuwamban 1967, ya bukaci musayar fili don zaman lafiya. Daga lokacin ne ake danganta yunkurin sasanta yankin da kudurin 242. An rubuta shi ne bisa la'akari da kuduri mai lamba VI na majalisar, a karkashinsa kuwa, kuduri shawara ce amma ba umurni ba.
Yarjejeniyar Camp David ta 1978
Wannan hoto da aka dauka a ranar 26 ga watan Maris 1979, na nuna shugaban Masar Anwar Sadat da takwaransa na Amurka Jimmy Carter da Firaminista Menachem Begin bayan rattaba hannu a Washington. Gamaiyar kasashen Larabawa, a karkashin jagorancin Masar da Siriya, sun yi fada a Yom Kippur ko yakin Oktoba a shekarar 1973. Yakin da ya jagoranci sulhu na kwanaki 12 da yarjeniyoyi biyu.
Taron birnin Madrid a shekara ta 1991
Amurka da tsohuwar Tarayyar Sobiet sun shirya taro a babban birnin Spaniya watau Madrid. Tattaunawar da ta kunshi Isra'ila da Jordan da Lebanon da Siriya da Palasdinawa, wanda shi ne karon farkon haduwarsu da tawagar Isra'ila, bai cimma wani abun azo-a-gani ba, sai dai ya tsara yadda tattaunawar gaba za ta kasance.
Yarjejeniyar birnin Oslo ta shekarar 1993
Tattaunawar wadda ta gudana a kasar Norway, tsakanin Isra'ila da kungiyar neman 'yancin kan Palasdinawa (PLO) ta samu nasarar cimma yarjejeniyar farko tsakanin bangarorin biyu. Ta bukaci janyewar sojin Isra'ila daga Gabar Yamma ta Kogin Jordan da Zirin Gaza da kuma kafa gwamnatin gashin kai. Gwamnatin rikon na Palasdinu na da wa'adin shekaru biyar na mulki.
Camp David shekara ta 2000
Shugaban Amurka Bill Clinton, ya gayyaci Firaministan Isra'ila Ehud Barak da shugaban Palasdinawa Yasser Arafat, domin tattauna batutuwan tsaro da kan iyaka da matsugunai da 'yan gudun hijira da kuma Birnin Kudus. Duk da tattaunawa fiye da na baya, babu abun da ganawar ta cimma. Rashin cimma matsaya a Camp David ne ya jagoranci sabon bore a bangaren Palasdinawa.
Shirin samar da sulhu na Larabawa a shekarar 2002
Tarurruka da dama sun biyo bayan tatttaunawar Camp David a biranen Washington da Alkahira da kuma Taba na Masar. Sai dai su ma babu wani sakamako. An sake gabatar da shirin sulhun na Larabawa a Beirut a watan Maris na 2002. Shirin ya bukaci Isra'ila ta janye a watan Yunin 1967, don samun damar kafa kasar Paladinu a Gabar Yamma ta kogin Jordan da Zirin Gaza. Su kuma Larabawa za su martaba Isra'ila.
Jadawalin 2003
Amurka da Tarayyar Turai da Rasha da Majalisar Dinkin Duniya sun yi aiki tare a matsayin bangarori hudu da ke aiki a kan jadawalin warware rikicin Gabas ta Tsakiya. A watan Yunin 2003, Firaminista Sharon da Mahmud Abbas na Palasdinu, sun amince da jadawalin, shi ma kwamitin sulhu ya amince a watan Nuwamba. Jadawalin ya tsara cimma yarjejeniyar karshe a 2005. Sai dai ba a aiwatar da shi ba.
Taron Annapolis a shekara ta 2007
A shekara ta 2007, shugaban Amurka George W. Bush ya dauki nauyin taron Annapolis, a Maryland, domin sake kaddamar da jadawalin sulhun. Firaminista Ehud Olmert da shugaban Palasdinawa Mahmud Abbas, sun halarci tattaunawar da bangarorin hudu da wakilan Larabawa. A nan aka cimma cigaba da tattaunawar da zummar cimma yarjejejiyar zaman lafiya a karshen 2008.
Tattaunawar Washington ta 2010
A shekara ta 2010, kokarin jakadan Amurka na musamman George Mitchell ya sa Firaministan Isra'ila Netanyahu ya amince da aiwatar da yarjejeniyar sulhun watanni 10 a yankunan da ake rikici. Daga bisani Netanyahu da Abbas sun amince da sake kaddamar da tattaunawar kai tsaye kan dukkan batutuwan. A watan Satumban 2010 aka fara tattaunawar, da bayan makonni ta watse.
Karuwar tashe-tashen hankula da tsagaita wuta
A karshen shekara ta 2012, an samu barkewar rigingimu a Gaza. Daga bisani aka cimma tsagaita wuta tsakanin Isra'ila da magabatan Zirin Gaza, har zuwa watan Yuni na 2014. Sai dai sabon rikici ya barke biyo bayan kisan gilla da aka yi wa wasu matasan Isra'ila uku bayan sacesu. Wannan ne ya sa Isra'ilar kaddamar da hare-hare da ya kawo karshen tsagaita wutar a ranar 26 ga Augusta na 2014.
Taron birnin Paris a shekara ta 2017
Jakadu daga kasashe sama da 70 ne suka hallara a birnin Paris na Faransa, domin tattauna rikicn da ke tsakanin Isra'ila da Palasdinawa. Netanyahu ya soki taron da cewar an nuna wa kasarsa son kai. Babu wakilan Isra'ila da Palasdinu a wajen taron. A wajen bude taron ministan harkokin wajen Faransa Jean-Marc Ayrault ya ce "mafita ita ce samar da kasashe biyu".