1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tarihin Ƙungiyar OPEC

May 19, 2011

Ƙungiyar OPEC da ta ƙunshi ƙasashe 12 masu albarkatun man fetur an kafa ta a shekara 1960

https://p.dw.com/p/11JvD
Tutar OPECHoto: Irani

OPEC Ƙungiya ce da ta haɗa ƙasashe masu albarkatun man fetur a duniya.

An ƙirƙiro ta ranar 14 ga watan Satumba na shekara 1960, wato yanzu shekaru 51 kenan da su ka wuce bisa shawara ƙasashen Venezuela da jamhuriya musulunci ta Iran.

Babban dalili da ya sa ƙasashe masu albarkatun man fetur yin tunanin ƙirƙiro OPEC shine su yi kariya ga faɗuwar farashen ɗanyan mai wanda a lokacin ake saida ganga ɗaya kan dalla Amurika biyar kacal.

wato har zuwa shekara 1970, kamfanonin da ke amfani da mai su ne su ke yankewa ƙasashe masu man farashe.To sai wani lokaci ƙasashen suka fahince cewar yanzu fa kan mage ya waye ,ba za su ƙara amincewa ba ana ci da gumunsu, wato duk da cewar suke da man, su ke haƙo shi, amma sai abinda kamfanonin da ke sanyan man su ka yi, su ka ce wannan ba zata saɓu ba, kaji dalilin da ya kai ƙasashen Iran da Venezuela shawartar sauran ƙasashe takwarorinsu, wanda kuma su ka basu haɗin kai, har aka girka OPEC, kluma tun bayan girka ƙungiyar ita ke da alhakin haudawa kokuma karya farashen mai sanan ita ke ƙayyade yawan man da ya kamata ko wace ƙasa memba ta haƙo a cikin shekara.

A lokacin da aka girka ta, Ƙungiyar OPEC na da membobin biyar kawai wato Saudi Arabiya,Jamhuriya musulunci ta Iran, Irak, Koweit da Venezuela.Sai daga bayane da dama daga ƙasashe masu albarkatun man fetur suka shiga a cikin ƙungiyar, inda a yanzu ta ke da membobi 12.Idan mu ka ɗauka dalla-dalla,a nahiyar Afirka akwai ƙasashe huɗu membobin OPEC Aljeriya,Libiya,Angola( ita Angola a baya bayanan ne ta shiga rukunin ƙasashen Opec yau shekaru biyar kacal kenan, kuma a Afrika baƙar fata, itace ƙasashe ta biyu bayan Najeriya wajen yawan albarkatun man fetur, an samu wani lokaci ma, inda ta zarta Najeriya fitar da ɗanyan mai a ƙetare dalili da rikicin da ya ɓarke a yankin Niger Delta, da Najeriya wadda ta shiga Opec yau shekaru 40 kenan da su ka wuce.

A Gabas ta tsakiya nan ne ke da ƙasashe mafi yawa, har guda shida wato Saudi Arabiya wadda itace ƙasar da ta fi ko wace yawan man fetur a duniya,sai Daular Larabawa, Irak, Iran,Koweit a Qatar.

Sai kuma yankin Latine Amurika akwai Equado da Venezuela.

Amma akwai wasu ƙasashe guda biyu wato Indonesiya da Gabon wanda sun taɓa zama memba a ƙungiyar OPEC amma daga baya suka fita dalili da ƙwahewar rijioyinsu na mai.

Indonisiya ta fita tun shekarar 1997 wato yanzun shekaru 14 kenan, a yayin da ƙasar gabon ta fita daga OPEC a shekara 1994 wato shekaru 17 kenan.

Idan wanda yayi tambayar ko Amurika memba ce a cikin Opec ya samu amsa a cikin tambayar da muka bada amsa yanzu, domin daga cikin ƙasashen da mu ka zana babu sunan Amurika.

Akwai ƙasashe da dama wanda suka mallaki albarakun man fetur amma ba su shiga cikin ƙungiyar OPEC ba, akwai Amurika,Kanada,Sudan,Mexique, Birtaniya,Nowe, Rasha da Oman.

Saidai ƙasashen OPEC su kaɗai su na samar da kusan kashi 50 cikin ɗari na man fetur da ake amfani da shi a duniya, sannan kuma sun mallaki kusan kashi 80 cikin ɗari na rijiyoyin man fetur na tsumi, wanda a yanzu ba a fara tunanin haƙar su ba.

A shekaru biyar na farko cibiyar OPEC na birnin Geneva na ƙasar Switzerland, daga nan aka cire ta aka maida ta birnin Vienna na ƙasar Austriya ranar ɗaya ga watan Satumba na shekara 1965.

Edita: Yahouza Sadissou Madobi

Mawallafi: Ahmad Tijani lawal