1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taron ƙungiyar EU kan ƙasar Girka

Abdourahamane HassaneMarch 25, 2010

Ƙasashen ƙungiyar Tarayya Turai na kokarin ceto ƙasar Girka da ga cikin halin da ta ke ciki na bashi

https://p.dw.com/p/McEi
Tutar ƙungiyar ƙasahen tarayya turaiHoto: EU

Na gaba ƙaɗan ne indan an juma da misalin ƙarfe biyar, fudu a gogon GMT shugabannin ƙungiyar ƙasashen tarayya turai zasu soma muhiman shawarwari da nufin samar da hanyoyin ceto ƙasar Girka, daga matsalar basusukan da suka yiwa ƙasar katutu, wanda kuma ke barazana ga faduwar daraja takardar kudin Euro a yankin na turai baki ɗaya inda har ba a yi hattaraba.Yanzu haka dai shugabannin ƙasashen na ƙungiyar na ta kokarin ganin yadda zasu ɓuloma lamarin,Shugabar gwamnatin Jamus Angela Mergel ta ce ta ƙudiri aniyar shawo kan abokanan hulɗa na ƙungiyar tarayya turai, harma da hukumar bayar da lamani ta duniya FMI domin taimakawa ƙasar girka da wani sabon tsari da zai iya bata damar ficewa daga cikin halin matsalar kundin da ta samu kanta a ciki .ƙasashe da dama na ƙungiyar tun da farko kamar su Faransa basu laminta ba a nemi agaji mayan bankunan na duniya domin magance matsalar ta ƙasar ta Girka suna masu cewa wannan wani abu ne da ke iya nuna kasawar ƙungiyar ta EU wajen magance matsalolinta.

Ana san ran a ganawar ta yau shugabanin ƙasashen na ƙungiyar ta EU zasu cimma dadaituwar baki da hukumomin na hukumar lamani ta duniya akan wani shirin taimakawa ƙasar girka da ƙudaden da zasu iya kai million 20 zuwa 30 na ƙudin Euro.

Mawallafi: abdourahamane Hassane

Edita : Tijani Lawal