Taron agajin duniya ya kan kama a Santambul
May 23, 2016Talla
Shugabanni na kasashen duniya na taruwa a birnin Santambul na kasar Turkiyya a ranar Litinin din nan a wani taron koli da ke zama na daban mai buri na ganin an kai ga samar da sauyi ga salon yadda ake tunkara kalubale da al'ummar duniya ke fiskanta sakamakon rikice-rikice da sauyin yanayi.
Fiye da shugabanni kasashe da ma na gwamnatoci 60 ne za su taru a taron kolin na kwanaki biyu bisa jagorancin Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Ban Ki-moon.
Kimanin mutane miliyan 60 ne dai suka samu kai a yanayi na raba su da muhallansu wasu kuma miliyan 125 ke neman su sami tallafi da kariya a fadin duniya, abin da dukkanin mahalarta taron suka amince da haka sai dai ya rage a ga rawar da za su taka wajen kawo karshen wannan tashin hankali.