Taron Annapolis kan Gabas Ta Tsakiya
November 25, 2007Talla
Shugabannin Isra´ila da na Falasdinawa sun isa a kasar Amirka gabanin taron kolin birnin Annapolis da za´a yi ranar talata da nufin farfaɗo da ƙoƙarin samar da zaman lafiyar yankin Gabas Ta Tsakiya. Yayin da ya yada ɗan gejeren zango a Washington shugaban Falasɗinawa Mahmud Abbas ya ce yana ganin taron wanda Amirka ta shirya a matsayin matakin farko na tattaunawar ƙarshe dangane da kafa wata ƙasar Falasdinu. Shi kuwa Firaministan Isra´ila Ehud Olmert cewa yayi yana sa rai za´a yi tattaunawa mai ma´ana.