Kokarin farfado da tatalin arziki a Masar
March 13, 2015Talla
Shugaban kasar Abdel Fattah al-Sisi dai na fatan taron zai taimaka wajen samun masu zuba jari na gida da na kasashen ketare a kasar. Rahotanni sun nunar da cewa tuni sakataren harkokin waje na Amirka John Kerry ya isa garin na Sharm El-Sheikh inda daruruwan 'yan kasuwa da sauran masu fada aji a duniya za su duba yiwuwar komawa huldar zuba jari da kasar ta Masar bayan tsahon shekaru hudu na tashin hankalin da take fuskanta. Sa'oi kalilan gabanin fara taron ma dai, sai da wasu kananan bama-bamai uku suka tashi yayin da wasu rokoki da aka harba a garin Sinai suka raunata sojojin kasar uku.