Alkawarin shuka itatuwa miliyan dubu a taron Davos
January 21, 2020Shirin wanda shugabannin shirya taron na birnin Davos da hadin gwiwar wani kamfanin inshura na birnin Zurich suka gabatar a taron na birnin Davos, na da nufin shuka itatuwa miliyan dubu dan ceton muhallin duniya.
Tuni dai shugabannin manyan kasashen duniya da suka hada da Shugaba Trump na Amirka suka kawo goyon bayansu ga shirin da ma aiwatar da shi ta hanyar kare dazuka a kasashensu.
Sai dai kuma masu fafutikar kare muhalli a duniya sun nuna shakkunsu a game da aniyar shugabannin kasashen duniyan na cika wannan alkawari a daidai lokacin da duniya ta zura ido ake ci gaba da kisan itatuwa ba kakkautawa a kurmin Amazon.
Batun kare muhalli duniya da rikicin Libiya da kuma na Gabas ta Tsakiya na daga cikin muhimman batutuwan da taron na Birnin Davos zai mayar da hankali a tsawon kwanaki hudu na gudanar da shi.