1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

G7. Sakon samar da zaman lafiya a duniya

Abdourahamane Hassane
May 19, 2023

Shugabannin kasashe bakwai masu arzikin masana'antu na duniya (G7) sun gana a kasar Japan.

https://p.dw.com/p/4RaBL
Themenpaket - G7 Summit Hiroshima Japan
Hoto: MINISTRY OF FOREIGN AFFAIRS OF JAPAN via REUTERS

A farkon taron kolinsu a Hiroshima, sun gudanar da bikin ajiye furanni na tunawa da wadanda harin bam din nukiliya na farko ya rutsa da su a yaƙin duniya na biyu. Shugaban gwamnatin Jamus Olaf Scholz ya bayyana cewa, tarihin birnin ya zama abin tunawa da alhakin da ya rataya a wuyan zaman lafiya da tsaro a duniya. An yi raga-raga da birnin na Hiroshima gaba daya a harin nukiliyar Amurka a watan Agustan shekara ta 1945, kafin harin bam na biyu na Atom bam da aka harba a Nagasaki inda mutanne mutane sama dubu dari suka mutu.

.