1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

G7 na taro a birnin Landan

Binta Aliyu Zurmi
May 4, 2021

Ministocin harkokin wajen kasashen G7 za su tattauna batun kalubalen da dimukuradiyya ke ciki da ma na hakkin al'umma.

https://p.dw.com/p/3svO6
Großbritannien Boris Johnson G7 Videokonferenz
Hoto: Simon Dawson/Avalon/Photoshot/picture alliance

A rana ta biyu a ganawar da ministocin harkokin wajen kasashe masu karfin tattalin arziki na G7 ke yi a birnin Landan na kasar Birtaniya, a yau za su tattauna batun 'yancin al'umma da ma barazanar da dimukuradiyya ke shiga a duniya a yanzu haka, a cewar sanarwar da offishin harkokin wajen Birtaniya ya fidda.Tattaunawar ta keke da keke da ake yin ta gabanin taron koli na kasashe mambobin G7 din da ke tafe a watan Yuni. Wakilan kasashen Amirka da Canada da Faransa da Jamus da Japan da ma Italiya za su gana da sakatare Dominic Raab na Birtaniya. Ana ganin batun juyin mulki a Myanmar na daga cikin manyan batutuwa da za su mamaye ganawar tasu ta yau, akwai batun Somaliya da rikicin Siriya da Libiya da kuma Habasha. Sanarwar ta ce taron ba zai tashi ba har sai sun kai ga tattauana batun ayyukan ta'addanci a kasashen G5 Sahel da ke yammacin Afirka.