1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Masar: Taron tantance bugun Al-Kur'ani

Mahamud Yaya Azare LMJ7RGB
September 28, 2021

A kokarinsu na tabbatar da ana yada ingantaccen bugu na Al-Kur'ani mai girma a duniya, kwamatin gyaran rubutun Al-Kur'ani na Al-Azhar ya yi zaman tantace bugun Al-Kur'anin da babu kurakurai cikinsa.

https://p.dw.com/p/40wig
Malaysia Kuala Lumpur  Royal Koran im Museum
Hoto: picture-alliance/Godong/F. de Noyelle

Wannan zama dai zai bayar da dammar ci gaba da buga Al-Kur'anai da babu kura-kurai da yadasu a duniya. Kwamitin gyaran bugun rubutun Al-Kur'anin na kasar Masar kan yi zamansa a duk lokacin da bukata ta taso, domin bai wa madabbabo'i da kasashe lasisin buga ingantaccen kwafin Al-Kur'anin da kwamatin ya tantance. Duk da cewa asalin haddar Al-Kur'anin ana dogara ne da lakantawa mai koyo da fatar baki, sai dai Sheikh Imad Muhsin ya ce shi ma rubutun na Al-Kur'anin na da nasa muhimmancin.

Bayan Al-Kur'anin da ake bugashi a takarda, kwamatin ya tsara wata manhajar Computer da ke iya gyara Al-Kur'anan da ake anfani da su kafar Internet da manhajojin koyar da haddar Al-Kur'ani mai girma, domin tabbatar da ganin cewa ba a koyar da yara ko masu koyo da Al-Kur'anin da akai kuskure wajen rubuta shi ba.