1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taro a Iran na duba makomar Siriya

Yusuf Bala Nayaya
September 7, 2018

Shugabannin kasashe uku na Iran da Rasha da Turkiyya sun fara taron koli kan makomar yankin Idlib na Siriya, yankin da ke zama sauran tungar 'yan tawaye masu adawa da gwamnatin ta Siriya.

https://p.dw.com/p/34Uco
Iran Teheran Syrien Gipfel - Putin trifft Erdogan
Hoto: Reuters/Turkish Presidential Palace/C. Oksuz

An dai bude zaman tattaunawar shugabannin ne a birnin Tehran na kasar ta Iran a wannan rana ta Juma'a. Shugaba Vladimir Putin na Rasha ya isa Tehran jim kadan bayan da takwaransa na Turkiyya Tayyip Erdogan ya sauka a kasar don halartar wannan taro da Shugaba Hassan Rouhani ke daukar bakuncinsa.

Putin ya ce 'yan tawayen sun buya a tudun mun tsira suna zagon kasa ga shirin tsagaita wuta.

Shugaba Erdogan dai na Turkiyya na dari-dari da ruwan bama-baman da dakarun Siriya da ke samun goyon bayan Rasha ke yi a yankin na Idlib wanda haka ka iya sanyawa a samu sabbin 'yan gudun hijira da za su iya shiga kasar ta Turkiyya daga iyakar kudanci.