1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taron kan rikicin Siriya

February 22, 2017

Masu ruwa da tsaki kan rikicin Siriya za su hallara a birnin Geneva na Switzerland da nufin sake tattauna batun tsagaita wuta a yakin da kasar ta kwashe sama da shekaru shida tana fama da shi.

https://p.dw.com/p/2Y3q9
Syrien Krieg - Kämpfe in Damaskus
Hoto: Reuters/B. Khabieh

A karshen watan Janairun da ya gabata aka sake samun sababbin kungiyoyi masu rajin jihadi a Siriya da ke da muradin kifar da gwamnatin Shugaba Bashar al-Assad na Siriya. Wadannan kungiyoyi sun hadar da "Syrian Conquest Front" ko kuma (Jabhat Fatah al-Sham) da "Army of the Fighters" ko kuma (Jayyish al-Mujahidin) wadanda kuma daga bisani suka hade tare da kafa wata kungiya mai suna "Organization for the Liberation of the Levant" (Hayyat Tahrir al-Sham, HTS).

Syrien Krieg - Kämpfe in Damaskus
Hoto: Reuters/B. Khabieh

Ita dai wannan sabuwar kungiya ta HTS tana rajin kwace iko da gwamnati da bangaren sojoji da ma siyasar kasar tare da kafa shari'ar Musulunci. Kungiyar ta HTS na daga cikin kungiyoyi da Rasha da Turkiya suka ce ba za a zauna kan teburin sulhu da su ba yayin tattaunawar da kasashen biyu suka assasa, wadda kuma ta gudana a Astana babban birnin kasar Kazakhstan. A yayin taron dai da Rasha da Turkiya da Iran suka jagorance shi, wanda kuma ya samar da tsagaita wuta an tattauna tsakanin bangaren gwamnati da na 'yan adawa, inda aka ki amincewa da kungiyoyi jihadi su shiga tattaunawar.

Kasachstan Syrien Friedensgespräche in Astana
Hoto: picture-alliance/abaca/A. Raimbekova

 

Gabanin taron na Geneva dai Faransa ta bukaci Rasha ta yi amfani da tasirin da take da shi a kan gwamnatin Shugaba Assad domin ganin an samu nasara a taron. Ministan harkokin kasashen ketare na Faransan Jean-Marc Ayrault ne ya bukaci hakan, inda ya ce kamata ya yi Moscow ta tilasta wa Assad ya daina yi wa baki dayan wadanda ke adawa da mulkinsa kudin goro ta hanyar kiransu a matsayin 'yan ta'adda. A cewarsa wannan wani abu ne da tilas ya kamata bangaren gwamnati su sanya a kwakwalwarsu in har za su yi magana da 'yan adawa domin tabbatar da ganin an samu sulhun da ake bukata. A daya bangaren 'yan adawar Siriya da aka amince su shiga cikin wannan  tattaunawa, sun nunar da cewa suna shirye kamar yadda shugaban hadakar kungiyar masu rajin juyin-juya hali da kuma adawa a Siriya Anas al-Abdah ya tabbatar.