Sabon shirin kare hakkin yara mata
November 16, 2021A wannan Talata aka bude taron kolin a birnin Yamai na 'yan matan Afirka. Taron kwanaki uku zai duba matsalolin da ‘yan matan Afirka ke fuskanta a rayuwa da suka hada da auren wuri da na dole ko kuma musamman tsautsayin samun juna biyu a lokacin da suke tsakiyar karatu, matsalolin da ke haifar masu da kyama a makarantu ko tsakanin sauran al’umma tare da tauye ‘yancinsu na samun ilimi. Karin Bayani: Mata sun yi zanga zanga kan fyade
Batun kare hakkin ‘yan mata 'yan boko wadanda suka ke fadawa tsautsayin yin ciki a makaranta ko kuma wadanda ake yi wa auren wuri ko na dole suna makaranta na daga cikin muhimman batutuwan da wannan taro na birnin Yamai zai duba. Kuma Mariama Mahamadou Chitou dalibar jami’a da ke halartar wannan taro ta bayyana irin kalubalen da ke a gaban ‘yan matan da ke tsintar kansu a cikin irin wannan yanayi na samun juna biyu a makaranta da ta ce, ya zama dole a shawo kan tarin matsalolin da ke kara yawaitar cin zarafin mata a sassan Afirka.
Ita ma Masaouda Maman daliba a makarantar sakanadare a birnin Yamai, ta bayyana karin wasu matsalolin kamar na yi wa mata kaciya ko auren dole da ke addabar ‘yan mata a rayuwarsu da kuma matakan da ya kamata iyaye da mahukunta su dauka domin tunkarar wadannan matsaloli a yayin taron. Za a dai share kwanaki uku ana gudanar da wannan taro, inda daga karshe ake sa ran fitar da shawarwari na kare hakkokin ‘yan mata da karfafasu, shawarwarin da za a gabatar a nan gaba ga taron koli na shugabannin Afirka.