Taron kasa na jam´iyar RDPC ta Kamaru
September 15, 2011Jam´iyar RDPC mai rike da ragamar mulki a kasar Kamaru ta buda babban zaman taronta a shirye-shiryen zaben shugaban kasa da zai wakana wata mai kamawa.
Shekaru 15 kenan cur, magoya bayan jam´iyar RDPC su ka share su na jiran jam´iyar ta ta kiri taron kongres din.
Shugaban kasa Paul Biya bugu da kari sugaban jam´iyar RDPC ya kiri taron na wannan karo a wani mataki na zabura da magoya bayansa, a daidai wannan lokaci na shirye-shiryen zaben shugaban kasa, da zai gudana a watan Oktoba mai kamawa.
Duk da cewar yakin neman zabe bai fara ba, amma a jawabin da Paul Biya ya gabatar ya bayana mahimman bururukan da ya ke bukatar cimma da zaran al´umar Kamaru ta sake zaben shi:
"Manyan bururukan da mu ke dauke da su baya, za su tabbata nan gaban kadan.Tun daga watan Janairu na shekara mai kamawa Kamaru za ta rikida domin za mu kaddamar da manyan gine-gine na ci gaban kasa".
Shugaban Pau Biya ya suka da kakkausar halshe ga yan adawa wanda ya ke zargi da yiwa yunkurin ci gaban kasa zagon kasa.
A cewar Alhaji Sani Yaro Matan haussa wani mai sharhi game da al´amuran siyasa a Kamaru, wannan taro na jam´iyar RDPC bai da wani amfani domin, shine ya kamata ya tsayar da takara shugaban Paul Biya, amma shugaban yayi riga malam massalaci ya ajje takara tun kamin taron ya yanke hukunci.
Shi kuwa Christophe Fomoniyo wani dan kasar Kamaru ne, wanda ke zaune a kasar Amurika, kuma ya ke jagorantar reshen Afrika a NDI wato kungiyar da ke kula da wanzuwar tsarin mulkin demokradiya a duniya, ya yi Allah wadai game da abinda ya kira koma bayan da Kamaru ke fama shi ta fannin demokradiya:
Oton:
"A baya-baya nan mun gani a kasar Kamaru, yadda aka yi wa kundin zabe kwaskwarima, inda aka kwacewa hukumar zabe ta ELECAM yaunin da ya rataya wuyenta, na bayyana sakamakon zaben wucin gadi.Wannan dokoki ne wanda su ka sabawa tsari irin na demokradiya"
Jam´iyar RDPC na kamalla taron ranar juma´a 16 ga watan Satumba, saidai a daya bangaren sauran jam´iyun siyasa mussamman na adawa sun fara korafi game da abinda su ka kira sale-salin magiudi da tuni gwamnati ta fara tanada domin shugaba Paul Biya ya yi tazarce.
Mawallafi: Yahouza Sadissou Madobi
Edita: Mohammad Nasiru Awal