1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taron kasashe makwaftan Libiya

September 1, 2021

A yayin kammala taronsu na kasashen da ke makwaftaka da Libya, an yi kira kan a janye mayakan kasashen waje daga kasar da ke arewacin nahiyar Afirka da rikici ya dai-daita.

https://p.dw.com/p/3zkvt
Algerien kappt Beziehungen zu Marokko
Hoto: Fateh Guidoum/AP/picture alliance

Taron na kwanaki biyu ya kuma bukaci Libiya ta kasance kan tafarkin siyasar kasar kana ta shirya zaben shugaban kasa da na 'yan majalisa a watan Disambar wannan shekarar.

Taron da ya gudana a Aljeriya ya sami halartar ministocin harkokin wajen kasashen Masar da Tunusiya da Sudan da Chadi da kuma Nijar, kasashen da suka kwashe shekaru suna nuna damuwarsu kan rikicin kasar ta Libiya.

A cewar ministan harkokin wajen Aljeriya Ramtane Lamamra, nasarar da za a samu a zaben ya ta'allaka ne kan janyewa sojojin hayar da ma wasu dakarun. Sai dai ya kara da cewa kasashen da ke makwaftaka da ita ka iya fadawa cikin hadarin da ta ke ciki idan har ba a gudanar da janyewar yadda ya kamata ba.

Libiya dai ta fada cikin rudani tun bayan tallafin da kungiyar kawancen tsaro ta NATO ta bayar ga rikicin da ya hambarar da gwamnatin shugaba Moammar Gaddafi a shekarar 2011, ya kuma raba ragamar gwamnatin kasar tsakanin gwmanatin da ke samun goyon Majalisar Dinkin Duniya a babban birnin kasar Tripoli, da kuma hukumomin da ke hammayya masu biyayya ga Khalifa Hafter a gabashin kasar.