1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taron kasashen G5 Sahel a Paris kan yaki da ta'addanci

Mohammad Nasiru Awal RGB
January 15, 2018

A wannan Litinin ministocin tsaro daga kasashe biyar na yankin Sahel sun gudanar da wani taro a birnin Paris a yunkurin karfafa girke rundunar yaki da ta'addanci a yankin mai fama da ayyukan kungiyoyin 'yan tarzoma.

https://p.dw.com/p/2qtAB
Taron shugabanin G5 Sahel da ya gudana a baraHoto: Reuters/L. Gnago

Ministocin tsaro daga kasashe biyar na yankin sun shirya taron bisa gayyatar takwarar aikinsu ta Faransa Florence Parly, a yunkurin baya bayan nan na karfafa girke rundunar yaki da ta'addanci ta G5 Sahel a yankin na Sahel mai fama da ayyukan kungiyoyin 'yan tarzoma da masu aikata muggan laifuka. Taron wanda baya ga ministocin tsaro da manyan jami'an soji suka hallara yana da burin sanya takamammen lokacin girke rundunar da ake wa lakabi da G5 Sahel wanda ta fara aikinta na farko a watan Nuwamban bara bisa tallafin kasar Faransa.

Kasashen Burkina Faso da Chadi da Mali da Mauritaniya da kuma Nijar suka hada kai da nufin samar da runduna mai sojoji 5000 da kuma za ta fara aiki a tsakiyar wannan shekara ta 2018 a yankin na Sahel da ya zama dandalin ayyukan tarzoma da kuma ke barazanar yaduwa zuwa wasu yankuna a cewar Dr. Dikko Abdoulrahmane na jami'ar birnin Zinder a Jamhuriyar Nijar kuma mai yin sharhi kan lamuran tsaro.

UN Mission MINUSMA
Rundunar MDD ta Minusma a yankin SahelHoto: picture-alliance/dpa/M. Kappeler

Rundunar G5 Sahel na da shirin yin aiki tare da dakarun Faransa da aka girke a Mali a shekarar 2013 hade da rundunar kiyaye zaman lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya wato MINUSMA a kasar ta Mali. Amman dukkan kasashen biyar na G5 Sahel da dukkansu Faransa ce ta yi wa mulkin mallaka, suna daga cikin mafiya talauci sannan rundunoni sojinsu ba su da isassun kayan aiki. To ko rundunar tana da dukkan abin da ake bukata na yaki da ta'addanci a yankin na Sahel?

Mali Bundeswehr Hubschrauber Tiger
Sansanin sojin Minusma a kasar MaliHoto: picture-alliance/dpa/Bundeswehr/M. Tessensohn

Paul Melly na cibiyar Chatham House da ke birnin London, manazarci ne a harkokin tsaro ya yi karin haske.
"Rundunar tana da aiki takamamme da za ta yi a yankin, inda aka girke dakarun kasa da kasa. Dakarun G5 Sahel za su inganta aikin wadannan dakaru, inda za su yi aiki a fadin yankin ga misali a yankunan kan iyakoki tsakanin kasashen Mali da Nijar da Burkina Faso. Kasancewa sojoji ne na wannan yanki, al'ummomin kasashen za su amincewa da su, kuma dakarun za su iya farautar 'yan ta'adda da ke kai hari a wata kasa sannan su tsere zuwa wata kasa."

Masana irin su Dr. Dikko Abdoulrahmane na masu ra'ayin cewa rundunar na da babban kalubale a gabanta. Amma idan ana son kwalliya ta biya kudin sabulu to dole a inganta musayar bayanai tsakanin masu ruwa da tsaki a sha'anin. Baya ga matakan soji ana kuma bukatar aiwatar da sahihan ayyukan raya yankin matukar ana son a samu nasarar dakile irin tasirin da 'yan ta'adda ke kara samu a yankin na Sahel.