Taro kan rikicin Gaza
November 11, 2023Ana gudanar da taron gaggawan ne makonni biyar bayan barkewar rikici tsakanin Isra'ila da kungiyar Hamas, wanda kawo yanzu ya yi ajalin mutane 1,200 a bangaren Isra'ila yayin da Falasdinawa 11,000 suka halaka ciki har da kananan yara kimanin 4,500.
Karin Bayani: Blinken ya kammala ziyara a Gabas ta Tsakiya da Asiya
Gabanin buda taron kamfanin dillancin labaran kasar Saudiyya ya bayyana cewa kasashen na son cimma matsaya guda daya a game da hatsarin wannan tashin hankalin da ba a taba ganin makamancinsa ba a zirin Gaza da yankunan Palastinawa ba.
Daga cikin mahalarta taron har da shugaban kasar Iran Ebrahim Raissi, kuma wannan ne ma ke zama karon farko da wani shugaban Iran din ke ziyarartar Saudiyya tun bayan kawo karshen zaman doya da man ja na shekaru bakwai tare da dawo da huldar diflomasiyya tsakanin manyan kasashen biyu na Gabas ta Tsakiya.
Dama dai a jajibirin buda taron Yarima mai jiran gado na Saudiyya Mohamed ben Salman a jawabinsa na farko a bainar jama'a kan rikicin na Gaza, ya yi Allah wadai da cin zarafin fararen hula da kuma keta dokokin kare hakkin bil adama na kasa da kasa da sojojin mamaya na Isra'ila ke yi a dan karamin yankin na Falasdinu.