Taron kasashen Turai kan Girka
March 18, 2015A gobe Alhamis da jibi Juma'a ce dai mambobin kungiyar za su hadu birnin Brussels na ksar Beljiyum don tattaunawa kan batun makashi sai dai matsalar da tattalin arzikin Girka ke fuskanta ce za ta kankane wannan taro du kuwa da ba shi ne makasudin kiran taron ba. An dai yi ta kai ruwa rana da shugabannin kungiyar da wasu mambobinta da ma kasar ta Girka kafin a kai ga amincewa da sanya batun na Girka cikin jerin batutuwan da taron maida hankali a kai.
Masu sanya idanu kan halin da ake ciki da ma kasahen da suka baiwa Girka bashi na ta aza ayar tambaya dangane da irin abinda ya sanya Girkan ke son a tattauna batutuwan da suka shafi bashin da aka bata da ma hali na masassara da tattalin arzikinta ya samu kansa a ciki. da ya ke tsokaci kan wannan batu Micheal Roth jami'i a ma'aikatar kudin tarayyar Jamus ya ce kyautuwa ya yi a maida hankali duba batutuwan da za su taimaka wajen fidda musu kitse daga wuta kan wannan batu.
Ya ce "kamata ya yi a tattauna kan batutuwan da za su taimaka wajen gyatta tsakanin EU da Girka. Ya kamata ne mu yi magana tsakaninmu ba mu maida hankali wajen yin maganganu a bayan fage ba".
Ita kuwa Mina Andreeva da zaman guda daga cikin masu magana da yawun cewa ta yi lokaci ya yi da za tattauna a ilimance don kaiwa ga matakin da ake son zuwa da nufin warware matsalar ta Girka.
Ta ce "yanzu lokaci ne da kwararru da kuma Girka ya kamata su zauna su tattauna kuma EU na bukatar ganin an samu cigaba cikin hanzari a irin gyare-gyaren da Girka ta yi alkawarin yi musamman ma ga kasashen da suka bata bashi."
To sai dai a daura da wannan, kasashe irin su Slovenia da ke cikin jerin wadanda suka bada basukan da aka baiwa Girka na son ganin Athens ta kai ga cika alkawura da ta dauka kafin a kai matsayin da al'ummar kasashen da suka bada basukan su fara yin tutsu. Firaministan Slovenia din Miro Cerar ya ce su ma suna fama da nasu matsin na basuka da kuma gibi na kasasfin kudi don haka bai kamata a ce an kai su bango ba a wannan gaba.
A kalamasu da ke kama da maida martani ga firaministan Slovenia kan batun na Girka, kwararru kan tattalin arziki na cewar Girka din na taka rawar gani musamman idan aka yi la'akari da rage kudaden da ta ke kashewa a lamuranta na yau da kullum da ma sauran matakai na daidaita tattalin arzikinta ko da dai sun ce ba lallai hakan ya dore ba. Nan gaba ne a cikin wannan watan awa'adin da aka debawa Girka din na biyan wasu basuka zai cika. Abin jira a gani dai shi ne yadda za ta kaya kan wannan batu mai sarkakakiyar gaske.