1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taron EU don dakile yaduwar corona

Abdoulaye Mamane Amadou
February 25, 2021

Shugabannin kasashen kungiyar tarayyar Turai sun gudanar da taroda zummar samun mafita kan gaggauta samun aklluran yaki da corona da ma yadda za a rarraba allurar rigakafin.

https://p.dw.com/p/3pwDF
EU-Gipfel Covid-19
Hoto: Olivier Hoslet/AP Photo/picture alliance

Shuwagabannin Kungiyar Tarayyar Turai sun soma wani taron kolinsu don tattauna batun yaki da annobar corona, wacce nau'u'unkanta da dama ke ci gaba da bazuwa a nahiyar.

Shugabbani na Turai na cikin rudani dangane da matakan da suka dace a dauka na dakatar da yaduwar cutar, tare da barin kan iyakokinsu a bude domin safarar kayayyakin bukatu na al'umma akarkashin tsarinsu na kasuwancin bai daya. 

Tuni dai shuwagabannin suka alkawarta samun karin alluarn rigakafin corona a zango na biyu na wannan shekarar, daga kamfanonin harhada magungua na Pfizer/BioNTech da kuma Moderna, tare duba yuiwuwar amincewa da allurar rigakafin kamfanin Johnson&Johnson a nahiyar.

Wakilan EU din 27 sun yi nazari kan takardar shaidar yin allurar rigakafin COVID, inda kasashen Turai na kudanci kamar Spain ke fatan hakan ne zai bude kofa ga masu yawon bude ido a wannan bazarar. Sai dai Faransa da Jamus da Belgium sun nuna damuwarsu dangane da wadanda wajibi ne su yi jira ko kuma su ki yarda da karbar allurar baki daya.