1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taron koli kan lafiya a kasar Yuganda

Ramatu Garba Baba
October 25, 2017

Wasu kasashen duniya akalla 50 za su soma taron koli kan lafiya a kasar Yuganda da zummar samar da hanyoyin dakile yaduwar cututtuka masu hadari ga lafiyar al'ummar duniya.

https://p.dw.com/p/2mUBf
DW Afrika Kodok Krankenhaus
Hoto: ICRC/Pawel Krzysiek

Taron da kasar Amirka ke jagoranta zai hada kan kungiyoyi masu zaman kansu da kuma wakilan wadannan kasashen don taimakawa kasashe dake fama da tsananin talauci tunkarar duk wata annoba da ka iya kunno kai har ta zama barazana ga lafiyar al'umma.

Za a yi anfani da wannan dama don wayar da kannun jami'an kiwon lafiya da kuma nuna musu alfanun sauyi a wajen inganta lafiyar al'umma, taron na gudana ne a yayin da aka samu bullar wata cuta mai yanayi da cutar Ebola a kasar ta Yuganda, mutum guda aka tabbatar da cewa ya kamu da cutar a yanzu.