An bude taron kolin Majalisar Dinkin Duniya
September 20, 2022Batun yakin Ukraine da Rasha da ya raba kan duniya, ya kasance babban batun da zai mamaye taron Majalisar Dinkin Duniya da aka bude a wannan Talata a birnin New York na kasar Amirka. Baya ga yakin Ukraine da ya janyo karancin abinci a duniya, kokarin kawo karshen fitar da hayaki mai gurbata iska da koma bayan Ilimi da barazanar da yunwa ke yi wa rayuwar mutum fiye da miliyan hamsin a yanzu, sun kasance cikin muhinman batutuwan da aka soma tafka mahawara a kansu a taron.
Shekaru biyu kenan, rabon da shugabanin su hadu wuri guda a sakamakon annobar corona inda aka koma gudanar da taron ta bidiyo, wannan ya sa majalisar, ta shawarci duk wani shugaban da ke da niyyar jawabi a zauren taron, da ya kokarta ya zo da kansa a maimakon bada jawabi ta bidiyo. Taron shi ne karo na 77 a tarihin majalisar.