1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shekaru 70 da kafuwar kungiyar tsaro ta NATO

Mohammad Nasiru Awal AMA
December 3, 2019

Duk da cikarta shekaru 70 da kafuwa da hakan ya sa shugabanninta halartar taron koli a birnin London, kungiyar tsaro ta NATO ba ta da wasu dalilai na yin kasaitaccen biki saboda tana fama da matsin lamba.

https://p.dw.com/p/3U9po
UK Nato-Treffen l US-Präsident Trump trifft NATO Generalsekretär Jens Stoltenberg
Hoto: Reuters/K. Lamarque

A gabanin taron cikar kungiyar NATO shekaru 70 da kafuwa ba a ga wani shirye-shirye na biki ba, wannan bai rasa nasaba da mawuyacin halin da kungiyar take ciki. Bayyana kungiyar da mai fama da mutuwar kwakwalwa da shugaban Faransa Emmanuel Macron ya yi a baya, ya sha suka a cikin kungiyar kawancen. Shugaban Faransa ya kuma yi kira ga samun karin 'yancin Turai kan batutuwan tsaro tare da yin gargadin cewa ba za  iya dogara da Amirka ba.

Kasashen gabashin Turai da dama sun soki lamirin shugaba Macron, kasancewa suna bukatar kariyar Amirka daga barazanar da suke fuskanta daga Rasha. Ita ma shugaban gwamnatin Jamus Angela Merkel ta soki kalaman inda ta ce:

"Turai kadai ba za ta iya tsaron kanta a yanzu ba. Mun dogara da hulda tsakaninmu da Amirka, saboda haka daidai ne idan muka ci gaba da yi wa wannan kawance aiki muka kuma dauki karin nauyi a kanmu."

Sukar sayen makamai daga Rasha 

Paris Macron und Stoltenberg
Hoto: AFP/B. Guay

Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya ba da hujjar yin kalaman ne da rashin samun hadin kai wajen daukar matakai na tsaro, inda ya yi nuni da harin da Turkiyya ta kai a kasar Siriya. Ba takaddamar da ke cikin NATO kawai ke bukatar karin tattaunawa tsakanin membobinta ba. Matakin da shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya dauka na sayen makamai daga Rasha abin dubawa ne. Shi ma Macron a makon da ya gabata ya goyi bayan a nemi taimakon Rasha don tabbatar da zaman lafiya da tsaro a Turai. Lamarin ya kuma sha suka a cikin kungiyar.

Donald Trump na nuna shakku 

Nato-Gipfel in London Donald Trump
Hoto: picture-alliance/dpa/E. Vucci

Shakkun da shugaban Amirka Donald Trump ke nunawa a NATO tare da yin kira ga sauran mambobin kungiyar da su kara yawan kudaden gudunmawa ga aiyukan kungiyar ya janyo rashin tabbas. Shi ma babban sakataren kungiyar tsaro ta NATO, Jens Stoltenberg ya ce yana da muhimmanci a kara yawan adadin kudin to amma ba don a dadada wa Donald Trump ba, yana mai cewa "Bai kamata kasashen Turai da Kanada su kara yawan kudin karo-karo ga NATO kawai don su dadada wa Shugaba Trump ba. Kamata ya yi su kara yawan kasafin kudi ga tsaro saboda sabbin barazana da kalubale da muke fuskanta, yanayin tsaro ya kara zama mai hatsari."

Ko shakka ba bu taron NATO a birnin London zai mayar da hankalim kan wasu batutuwa na dabam, kamar aikace-aikacenta a sararin samaniya da dangantakarta da kasar China. Sai dai wadannan batutuwa za su koma sahun baya saboda rikicin cikin gida da take fama da shi.