Taron kula da harkokin tsaro na Munich
February 2, 2013Bayan kasashe dake samun bunkasa yanzu, kamar Brazil da Chna, suma kasashen Afrika suna daga cikin wakilai 400 daga kasashe fiye da 70 da zasu halarci tzaron na Munich tun daga daya zuwa uku ga watan Fabrairu masu bunkasa. Tuni kuma, wannan taro ya zama ba matattara ta yan siyasa bane kadai. Suma masana tattalin arziki da wakilan kungiyoyi masu zaman kansu sukan hahllara domin shiga tattaunawar da akan yi. Hakan dai ya maida taron tsaron na birnin Munich a matsayin wani dandali na nazari da kuma duba canbje-canjen al'amuran tsaro a duniya baki daya a karni na 21, inda bayan batun tsaro da yadda za'a fuskanci sabon zamani na yaki ta amfani da yanar gizo, za'a kuma yi nazarin batun canjin yanayin sararin samaniya.
Taron zai kuma tattauna batun kasuwanci tsakanin ƙaasahen
Duk kuma da taruka masu yawa da ake amma ana ci gaba da samun karuwar massu bukatar halartar tarojn na tsaro a Munich. Wakilai dabam dabam har kimanin 90 ne zasu hallara a zauren taron. Tawagar da babu shakka zata fi daukar hankali ita ce wadda mataimakin shugaban Amerika, Joe Biden yake wa jagoranci. Mataimakin shugabanna Amerika ya taba halartar taron na Munich a shekara ta 2009, inda ya gudanarda jawabi a game da dangantakar dake tsakanin Amerika da Rasha. Tun kafin ya isa birnin na Munich sai da Biden ya yada zango a Berlin, inda ya gana da shugaban gwamnati, Angela Merkel. Daga baya, ta shaidawa manema labarai cewa:
Mun tattauna a game da batun daidaita al'amuran kasuwannin hada hadar kudi na duniya, mun tattauna a game da al'amuranda suka shafi manyan kasashen duniya bakwai masu karfin tattalin arziki da rukunin kasashe ashirin masu ci gaba, muna kuma aiki tare da hadin kai kan manufofinmu na tsaro, musamman a game da yakin da muke yi a Afghanistan da kuma yaki da aiyukan tarzoma a duniya baki daya.
Ziyarar da mataimakin shugaban na Amerika, Joe Biden ya kai Berlin, jim kadan bayan da aka rantsar dashi karo na biyu kan wnanan mkami, wata alama ce ta kyakkyawar dangantakar dake tsakanin kasashen biyu. Bayan al'amura na siyasa da tsaro, shugaban gwamnati, Angela Merkel da ministanta na harkokin waje, Guido Westerwelle ysun dade suna kokarin ganin an sami wata yarjejeniya ta ciniki da kawar da fito a kayaiyakin da kasashen suke sayarwa junan su. Shi kansa a lokacin wannan ziyara Joe Biden ya kwatanta Jamus a matsayin kawa kuma abokiyar hadin gwiwa ta hakika.
Manyan kalubalan da ke a gaban taron sune na tabbatar da zaman lafiya
Jamus kasa ce da zata ci gaba da kasancewa mai matukar muhimmanci a dangantaka tsakanin kasashen Turai da Amerika, kuma kasar da ta zama tushen da muka dora dangantakar su da sauran duniya baki daya a kansa, wanda kjma idan ba tareda nahiyar Turai mai karfi ba, yana da wuya mu iya hangen yadda dangantakar Amerika zata kasance da sauran duniya.
A wannan shekara, karon farko, daga cikin masu halartar taron na Munich har akwai ministan harkokin wajen Brazil da kuma babban mai gabatar da masu laifi a kotun kasa da kasa a birnin Hague. Manyan al'amuran da taron na bana zai maida hankali kansu, sun hada har da rikice-rikicen da ake fama dfasu a Mali da Syria da kuma yadda za'a yi da Iran.
Mawallafi : Umaru Aliyu
Edita : Usman Shehu Usman