BRICS: Yawan mabobi domin ci-gaba
August 24, 2023Shugabannin kungiyar Kasashen da Tattalin Arzikinsu ke Bunkasa wato BRICS da suka hadar da Brazil da Rasha da Indiya da Chaina da kuma Afirka ta Kudu, sun tattauna tare da amincewa da batun karbar sababbin mambobi a kungiyar a kokarin da take na samun karfin fada a ji a duniya.
Tun da fari dai an samu sabani a tsakaninsu, inda Indiya ta nuna kin amincewarta. Sai dai daga bisani, Indiyan ta bayyana cikakken goyon bayanta na samun karin mambobin da rahotanni suka ce kasashe kimanin 40 sun mika bukatunsu na shiga kungiyar.
Kungiyar ta BRICS ta amince da kara mambobi shida, wadanda suka hadar da Ajantina da Masar da Iran da Habasha da Saudiyya da kuma Hadaddiyar Daular Larabawa. Tarayyar Najeriya dai, na daga cikin kasashen da aka yi fatali da bukatarsu ta shiga wannan kungiya da ke shirin yin gogayya da sauran kungiyoyi masu fada a ji a fannin tattalin arziki a duniya.