An kammala taron kasashe masu arziki na G20
September 5, 2016Talla
Shugabannin kasashen duniya masu karfin tattalin arziki na kungiyar G20 da suka kammala taro a birnin Hangzhou na gabashin China, sun amince da fuskantar kalubalen bunkasar tattalin arziki da inganta muhalli.
Shugabar Asusun Ba da Lamuni na Duniya, IMF, Christine Lagarde ta ce matsaya kan bunkasa tattalin arziki da aka amince yayin taron shugabannin kasashen na G20, dole a tabbatar da ya kunshi duk kasashen duniya. Sannan ta bukaci kasashen wajen zage damtse kan aiwatar da sauye-sauye gami da manufofi maimako su kare kan takarda.
Wani abu mai muhimmanci shi ne kara samun bunkasa a nahiyar Afirka wadanda mutanenta ke karuwa cikin gaggawa. Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta ce tuni aka dauki matakin kara zuba jari a wannan nahiya.